✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don Uwargida: Lakanin Zama Da Miji!

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta more zama…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta more zama da maigidanta. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Yadda Za ki Zauna Da Mijinki: A cikin Aya ta 34 cikin Suratul Nisa’i, Allah SWT Ya bayyana mana siffofin mace ta kwarai:

“…Salihan mata, masu da’a ne, masu tsare gaibi saboda abin da Allah Ya yi umarni a kiyaye.”
Wadannan siffofi guda biyu: da’a da tsare abin da Allah Ya yi umarnin a tsare, su ne sinadaran zama da miji; su ne lakanin da za ki yi amfani da su don ki zama matar da mijinki zai rika so a kullum; su ne siffofin salihar mace, wacce Manzon Allah SAW Ya siffanta da mafi kyawu. Idan kina so ki zama haka ga maigidanki ya ’yar uwa sai ki yi kokari ki cika wadannan kyawawan siffofi na macen kwarai, kamar yadda Allah SWT Ya bayyana, domin Shi Ya halitta ’ya mace, Ya fita sanin mafi kyawun abin da zai kyautata na daga dabi’a da yanayin zamantakewa. Don haka sai ki yi amfani da wadannan sinadaran kamar yadda bayaninsu zai zo:
da’a: Yin da’a ga maigida ba yana nufin yi masa ladabi da biyayya kadai ba, duk da cewa suna ciki; yin da’a ga maigida ya kunshi har da salo-salon bayyanar da soyayya gare shi, da yi masa abubuwan jan hankali. Ki lura da yadda kayan sarrafa sha’awa na mata ake masu lakani da ‘kayan da’a.’ Ga bayani kan ire-iren da’ar da za ki rika yi wa maigidanki, musamman a wannan lokaci na bankwana da masoyin wata na Ramadan da kuma gabatowar shagalin Sallah, don ya kasance kin ribaci dimbin ladan da ke ciki:
1.    Ladabi Da Biyayya: Wannan shi ne tozon da’ar da za ki yi wa maigidanki, duk wata da’a da za ki yi masa, idan har ba ki yi masa ladabi da biyayya ba, to wannan da’a za ta zama mai nakasu kwarai da gaske. Amma in kina masa ladabi da biyayya, ko da ba ki yi masa sauran bangarorin da’a ba, ladabi da biyayya na iya sakaya inda kike da rauni har ba za a lura ba ki yin su ba ma.
Ladabi- shi ne yin amfani da hankali wajen kiyaye duk abin da kika san maigidanki ba ya so, sannan ki rika yin hakuri da tausasa zuciyarki wajen bin dokokinsa sau da kafa; sannan yana daga cikin ladabi ki rika girmama mijinki da kankan da kai gare shi, rashin raina shi ko raina kokarinsa; rashin yi masa rashin kunya da gaya masa bakaken maganganu. Ladabi ne danne zuciyarki yayin da ya bata miki rai da nuna fushinki gare shi ta hanya mafi sauki.
Biyayya- ita ce bin umarninsa kodayaushe cikin halin kunci da na dadi, amma wannan a cikin umarnin da ba su saba wa dokokin Allah SWT ba. Kamar yadda Hausawa ke cewa: “yi na yi, bari na bari ta raba ka da kowa,” idan kika zama mai biyayya sau da kafa ga mijinki, to za ku zauna lafiya, ba za a taba jin kanku ba. Ki sani ya uwargida, ke ce ya dace ki yi masa biyayya, domin shi ne shugabanki, kina kasa da shi, kuma ke mallakinsa ce, don haka kada ki dauka cewa yin haka kaskanci ne gare ki, a’a, yin ladabi da biyayya babbar daraja ce gare ki, kuma ita ce cikar kamalarki ta ’ya mace.
Duk macen da ba ta da ladabi da biyayya, to za ka tarar dabi’unta sun fi kama da na dabbobi sama da na mutane. Kuma idan kika iya sarrafa makaman kashe lakar da namiji da Ubangiji Ya hore miki, sai ya zama mijinki yana miki ladabi da biyayya ba tare da wai kin umarce shi da hakan ba, ko kin sa masa wasu dokoki.
2.    da’ar So Da kauna: Uwargida za ki yi wa maigidanki da’ar so da kauna iri biyu: na farko shi ne, ki yi tanadin so mai dumi da sahihiyar kauna cikin zuciyarki game da mijinki, hadi da sauran kyawawan shau’ukan ’yan rakiyar shau’kin so da kauna. Sannan sai ki rika bayyanar da wannan so da kaunar salo-salo a zahirance. Za ki yi haka ne ta hanyar jiji da shi, shagwaba shi da yi masa shagwaba, sannan kallonki da murnushinki gare shi su zama masu cike da so da kauna da jan hankali. Kin fi kowa sanin irin makaman jan hankalin da Ubangija ya ni’imta ki da su, don haka sai ki yi amfani da su wajen samun ladar auren ki wanda shi ne rabin addinin. Ki sani cewa, so, kauna da ingantacciyar kulawa ga juna su ne dadin rayuwar aure ba dukiya, daula da more rayuwar duniya ba. Don haka kodayaushe ki zama mai yawan sabunta salo-salon so da kaunar da za ki rika bayyanarwa ga maigidanki; ki yawaita yin masa abubuwan jin dadin da za su faranta masa rai. Haka kuma ki zama mai yawan sabunta soyayyar auren ku ta hanyar yi masa abubuwan da ba ki taba yi ba, ki nemo sababbin hanyoyin kayatar da shi da sauran duk abubuwan da kika san sun dace da maigidanki ta wannan bangaren.
3.    da’ar Hakuri da Sadaukarwa: Yana daga cikin dabi’un yin da’a ga maigida yawan yin hakuri da shi da halayensa; don haka uwargida ki tausasa zuciyarki, ki zama mai yawan yin hakuri da maigidanki a kodayaushe; komai runtsi kuma komai tsanani kada ki gajiya kuma kada ki daina, domin shi hakuri wani abu ne da ba shi da iyaka, kuma duk ranar da kika ji kin gaji da yin hakuri, wannan rashin hakurin na rana daya sai ya bata wancan na bayan ya zama kamar ba ki yi shi ba. Haka kuma yana daga cikin da’ar da za ki yi wa maigida, wato ki rika yawan sadaukar da bukatunki domin nasa.
4.    da’ar Yabo da godiya: Yawan godiya da yaba wa kokarin maigida dangane da duk abin da ya kawo na bukatar gida, ko wani aiki da ya gabatar, komai kankantarsa, to a gode masa, a yaba masa, kuma ki bayyana masa jin dadinki. Kada ki dauka dole-dolensa ne kulawa da ke, wannan irin halayya na sa magidanta su rage kaimi wajen kyautata kulawarsu ga iyalansu. Ki sani, kamar yadda ya zo a wani ingantaccen Hadisin Manzon Allah SAW, halin wasu matan na rashin yin godiya ga mazan auren su shi ne, sanadiyyar halakarsu ranar lahira.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe.