Ka gabatar da kanka a takaice?
An haife ni a yankin Getsi da ke Unguwar Tudun Murtala, karamar Hukumar Nasarawa a cikin birnin Kano. Na halarci makarantar Islamiyya da ke hade da Firamare mai suna Bahrunnada, daga nan na tafi sakandiren gwamnati da ke titin Tudun Wada a Sabon Garin Kanon mai suna (KGC). Bayan nan na tafi Kwalejin Nazarin Shari’a da Addinin Muslunci (AKCILS) wacce aka fi sani da Ligal inda na karanta Dokokin Zamani (Cibil Law) kuma na samu shaidar difloma akan hakan. Daga nan sai na tafi Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) inda na karanta kimiyyar harshe (Linguistics) kuma na sami shahadar digiri na daya (B.A). A halin yanzu na fara shirye-shiryen tafiya kasar Amurka domin fara karatun digiri di na biyu a kan fassara, da izinin Allah.
Na shiga harkar siyasa sosai, inda duk da karancin shekaruna jam’iyyar AC suka zabe ni a matsayin Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar a mazabar Tudun Murtala wanda na ajjiye daga baya saboda wasu dalilai. An kuma nada ni a matsayin Babban Sakataren kungiyar daliban karamar Hukumar Nassarawa (NALSA) reshen kwalejin Ligal, da kuma Sakataren Kudi na kungiyar dalibai Masu Nazarin Kimiyyar Harshe ta kasa (NALLS) reshen Jami’ar Bayero. Kuma an nada ni a matsayin Mataimakin Shugaban Zauren Marubuta na kungiyar dalibai Musulmai ta kasa (MSSN) reshen Jami’ar Bayero. Haka kuma an zabe ni Shugaban NALLS reshen Jami’ar Bayero. A yanzu kuma nine zababban mai bada shawara a fannin shari’a ga kungiyar Marubuta ta kasa (ANA), reshen Jihar Kano.
Ina da lambobin girmamawa guda biyu, daya daga masu bautar kasa (NYSC) a Jihar Kano a shekarar 2017 mai taken “Lambar Girmamawa Ta Zakakuranci” dayar kuma daga kungiyar daliban Jami’ar Bayero (SUG) mai taken “Shugaban dalibai Na Sashe Da Ya fi Kowani Shugaba Yin Aiki Ga dalibansa a BUK a Shekarar 2017”
Mene ne tarihi kamfanin fassara na Sunrise Languege Practioners (SLP)?
Na kafa kamfanin SLP a shekarar 2017 inda na kama hayar ofis a No.8B Zoo road Kano a saman bankin Uniyon kusa da gidan man Total. Na dauki ma’aikata masu kwarewa da kuma digiri digiri daga jami’oin gida Najeriya da na ketare a fannonin harsuna daban-daban wato harsunan Hausa da Turanci da Larabci da Faransanci da Indiyanci da Cananci. Biyu daga cikinsu suna da mataki mai daraja ta daya (First Class) a shaidar digirinsu. Wasu daga cikin ma’akatan SLP din kuma tuni sun kusa kammala digirinsu na biyu a dai fannikan harshen da suka yi digirin farkon. Bugu da kari, a cikin ma’aikatan akwai dalibin da yake karanta Harshen Hausa a Kwalejin Horar da Malamai (FCE) ta Kano, da wani kuma da yake karanta Kimiyyar Harshe a matakin digirin farko da kuma daya da ya yi karatun difloma a FCE din ta Kano. Muna da sakatariya wacce ita ma digiri ne da ita daga Jami’ar Bayero. Ba akan tsarin albashi na dauki ma’akatan aiki ba, na daukesu ne a kan tsarin idan sun yi aiki su samu kudinsu, amma ita sakatariya saboda kullum daga Litinin zuwa Juma’a take zuwa daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma ita kadai ce take da albashi, ko nima bani da albashi a matakin yanzu, sai aiki ya samu sannan ni da sauran ma’aikan SLP muke samun kudi.
Lauyan kamfanin mu shi ne Rabi’u Sadeek BK Esk da ke ofishin lauyoyi wato danyaya Chambers Kano.
Farfesa Hafizu Miko Yakasai, Shugaban kungiyar Masu Fassara da Tafinta ta kasa (NITI) da Farfesa Bashir Sambo da Malam Muhammad Sulaiman, dukansu malaman harshe ne a Jami’ar Bayero, sun zo sun yi wa dukan sababbin ma’aikatan SLP horo na kwana biyu, kamar yadda kamfanin ya shirya domin kara gogar da ma’aikatansa don su rika yin ayyuka masu inganci sosai, kuma SLP zai rika gabatar da ire-iren wannan horon da bita da taron karawa juna sani lokaci zuwa lokaci ga ma’aikatansa.
Wane ayyuka kuke yi baya ga fassara da tafinta?
Ayyukan da kamfanin SLP yake sun hada da fassara da yin tafinta da juya sauti zuwa rubutu da fassara hirar fim a rubuce da juya rubutu zuwa sauti da tace rubutu da yin rubutun jawabi da gabatar da bita da gabatar da taron karawa juna sani da Koyarwa da rubuta labarin fim da rubuta tarihin rayuwar mutum, da sauransu.
Duka wadannan ayyukan muna yinsu a cikin harsuna shida da na ambata da ma harshen da ban ambata ba.
Me ya ja hankalinka har ka yi tunanin assasa wannan waje?
Abubuwa 5 ne suka ja hankali na na kafa wannan kamfanin, kuma su ne: Ayyukan harshe da ake ba ni kuma nake yinsu a gida sannan abokanan huldar tawa sai na ga suna jin dadi kuma suna yaba aikin. Da darasin koyar da dogaro da kai (EEP) da Farfesa Sagagi da ‘yan tawagarsa suka koyar da mu lokacin muna jami’a. Da jawabin da na gabatar ga kungiyar dalibai Musulmai ta kasa (MSSN) reshen Jami’ar Bayero shekaru biyu da suka wuce mai taken “Rubutu: Fasaha kuma Sana’a”. Da kuma son kawo sauyi a fannin ayyukan harshe, domin wasu lokutan za ka rika ganin kura-kurai masu cin zarafin harshe a fassara da rubutun talla da fassara hirar finan-finan Hausa da sauransu.
Wane buri kake son cimmawa?
Da izinin Allah, SLP na son cimma burin zama zakaran gwajin dafi a Najeria, Afirka da ma duniya baki daya. Manufar mu kuma ita ce yi wa abokanan huldarmu ayyuka masu ingancin gaske tare da girmama alkawarin lokacin kammala aiki da muka yi dasu da kuma daraja su.
Wane kalubale kuke fuskanta?
Rashin wadataccen jari shi ne babban matsalar da nake fuskanta, amma ina godewa Allah saboda da ‘yan dubu daruruwa na da basu kai miliyan daya ba na fara wannan harkar amma kuma gashi sai ci gaba muke samu ta yadda aikin farko da muka samu a a shekarar nan daga Jami’ar Kolons ne da ke kasar Jamus sai kuma wasu ayyukan suma dai da muka samu bayan wannan. A halin yanzu kuma muna yin wani aiki da muka samu daga kwalejin Ligal. Yadda kaina ke yin zafi shi ma wani kalubale ne da nake fuskanta saboda kafa kamfani na kwararru kamar nawa koda kana da wadataccen jari ba karamin jan aiki bane. A duk mako nakan yi ciwon kai sau daya ko sau biyu saboda wahalhalun gudanar da kamfanin nan. kalubale na karshe da zan ambata shi ne duk da kokari da muke yi muna yin ayyukan masu inganci, riba da muke samu yanzu kadan ce wadda idan ka kamanta ta da ta wasu kamfanin takwaririnmu, babu shakka ba ka yi karya ba idan ka ce kyauta-kyauta muke yin ayyukanmu. Duk da cewa muna da tsayayyen farashi a hukumance na kowanne daga cikin ayyukanmu, wadanda dukansu da Dalar Amurka muke lissafin saboda a ka’idar kasuwar aikin harshe a ko ina a fadin duniya, da dala ake tsayar da farashi.
Yaya za a magance matsalolin?
Samun karin jari. Yanzu haka na hakura da kudin da nake samu a matsayin riba ina kara saka shi a cikin kamfanin ta hanyar sayo abubuwan da ban sayo ba da kuma canza wasu da dai sauransu, sannan kuma na nemi tallafin kudi daga YOUWIN da makamantansu, uwa uba kuma shi ne na ci gaba da hakuri sannan ina kuma ina ba ma’aikata na hakuri da riba kadan mai albarka a tsawon shekara daya zuwa biyun farko kafin daga bisani kuma kowa a kamfanin ya fara samun madudan kudade.
Yaya kake ganin matsalar rashin son karance-karance musamman a Arewacin Najeriya?
Gaskiya matsalace babba, domin duk al’ummar da ba ta damu da karance-karance ba sai domin jarrabawa, kamar dai al’ummar Arewacin kasar nan dama kuma na kasar baki daya, zaka ga cewa jarrabawar take ci kawai amma babu fahimtar ainihin karatun yadda ya kamata. Wannan ne ya sa za ka ga likitoci suna kashe marasa lafiya, injiniyoyi suna zana gidaje marasa karko wadanda bayan an gina suke ruguzo wa mutane su kashe su, malaman makaranta suke kasa cin jarrabawar tantancewa, dalibai a kowane mataki suke ta satar amsa a lokacin jarrabawa, da dai sauransu duka saboda rashin dabi’ar karance-karance.
Meye kiranka ga gwamnati game da yadda za a taimaka wa harkar adabi?
Gwamnatoci a kowane mataki na mulki su kawar da yunwa a tsakanin al’ummar su domin ci yana gaba daga karance-karance da kuma karatu. Babu yadda za a yi mutum bai koshi ba, har ya yi tunanin karanta littattafansa na makaranta balle har ya yi wani karance-karance. Bayan talaka ya koshi, sai a tilasta koyar da darasin adabi (Literature) tun daga makarantun Firamare domin babu wata hanya ta koyawa dalibi da kuma gina masa dabi’ar karatu da ta wuce koyar da shi darasin adabi.