Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ta umarci Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da sauran ministocin da ke zawarcin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 su ajiye mukamansu nan da ranar 16 ga watan Mayun da muke ciki.
Minsitan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, shi ne ya sanar da hakan bayan zaman Malisar Zartawar ta Tarayyar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagornta ranar Laraba a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Yadda takarar ministoci ke shafar ayyuka a ma’aikatun gwamnati
- Bom ya tashi a kusa da barikin sojoji a Jalingo
Umarnin ya shafi duk wani mamba a Majalisar Zartarwa ta Tarayya da ke neman takara a zaben 2023, ciki har da Ministan Kwadago da Kyautatuwar Aiki, Chris Ngige.
Sauran su ne Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajiuba; da Minista a Ma’aikatar Mai, Timipre Sylva, masu neman takarar shguaban kasa.
A kwai kuma Ministan Kimiyya da Fasa, Ogbonnaya Onu da kuma Ministan shari’a Abubakar Malami da ke neman takarar Gwamnan Jihar Kebbi.
Karin bayani na tafe…