✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a janye karin kudin mai da wuta —’Yan kwadago

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ce ba gudu ba ja da baya a shirinsu na tsunduma yajin aiki sai idan gwamnatin ta janye karin farashin…

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ce ba gudu ba ja da baya a shirinsu na tsunduma yajin aiki sai idan gwamnatin ta janye karin farashin mai da na wutar lantarki ba.

’Yan kwadago karkashin jagorancin kungiyoyinsu NLC da TUC sun jaddada matsayin nasu ne yayin tattaunawarsu da Gwamnatin Tarayya a Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis.

Kungiyar NLC dai ta ba gwamnatin wa’adin mako biyu kan ta soke karin ko ma’aikata su tsunduma yajin aikin daga ranar Litinin 28 ga watan Satumba.

Matakin na zuwa ne bayan wani zama da kwamitin zartarwar ’yan kwadago ya yi a kwanakin baya.

Yayin tattaunawar ranar Alhamis, an yi zaton gwamnatin za ta fayyace wasu tsare-tsaren rage radadi.

To sai dai majiyoyinmu sun ce gwamnatin ba ta zo da wani kwakkwaran tsari ba ga ’yan kwadagon, ballantana ragowar ’yan Najeriya.

Wasu na ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin halin tsaka mai wuya na tattalin arzikin da gwamnatin ke cewa ta tsinci kanta a ciki.

Rahotanni dai sun nuna cewa muhawara ta yi zafi tsakanin gwamnati da ’yan kwadagon a wata tattaunawar da za a iya cewa ba ta haifar da da mai ido ba.

Yayin da gwamnatin ta kekashe kasa cewa za ta fito da matakai da hanyoyin rage radadi ga ’yan kasa, ’yan kwadagon dagewa suka yi sai an koma kan tsohon farashi muddin ana son maslaha.

Wakilan gwamnati a tattaunawar sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Minista a Ma’aikatar Man fetur, Temipre Sylva; Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman; Ministan Kwadago, Chris Ngige; Minista a Ma’aikatar Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo; da dai sauransu.

Daga bangaren ’yan kwadagon kuwa, Shugaban NLC, Kwamaret Ayuba Wabba da takwaransa na TUC Kwamaret Quadri Olaleye ne suka wakilci ma’aikatan Najeriya.

To sai dai a ranar Alhamis Kotun Sasanta Rikicin Ma’aikata ta ba da umarnin na wucin gadi na dakatar da kungiyoyin kwadagon daga yunkurinsu na shiga yajin aikin.

Kotun, karkashin Mai Shari’a Ibrahim Galadima ta umarci kungiyoyin da su yi biyayya ga umarnin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci na karshe kan lamarin.