✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dole a biya diyyar mutanen da aka kashe a Jos, a hukunta masu laifi’

Kungiyar ta kuma ce dole a zakulo masu hannu a rikicin tare da hukunta su.

Wata kungiya mai fafutukar kare hakkin bil-Adama da ke Kano (HRN) ta ce ya zama wajibi Gwamnatin Jihar Filato da ta Tarayya su biya diyyar mutanen da aka kashe a garin Jos a kwanakin baya.

Kungiyar ta kuma ce dole a zakulo masu hannu a rikicin tare da hukunta su kamar yadda ya kamata domin kare faruwar hakan a nan gaba.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta, A. A. Haruna Ayagi, HRN ta kuma nuna takaicinta kan yadda ake ci gaba da kashe ’yan Najeriya, ciki har da na kwana-kwanan nan da jami’an Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (Kwastam) suka yi a Jibiya a Jihar Katsina da kuma a Jihar Kano.

Sanarwar ta ce, “Wannan kungiya na jaddada kira ga Gwamnatin Najeriya da hukumomi a Jihar Filato, da su biya diyya ga magada da ’yan uwan wadanda a ka kashe, sannan ba tare da bata lokaci ba, su hukunta wadanda su ka aikata kisan.

“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da sauran masu damara cewa su daina amfani da matsayi ko kaki wajen cin mutuncin jama’a.

“Wannan kungiya na bayyana matukar takaicinta da damuwa da irin yadda a ke karkashe jama’ar kasar nan da ba su ji ba, ba su gani ba, ko dai da sunan rikicin addini da na kabilanci, ko sanadin ayyukan  rashin kan gado daga wasu jami’an tsaro.

“Duba da abin da ya faru kwanan nan, inda jami’an Kwastam suka haddasa hadarin da ya lakume rayukan mutane a Jihar Katsina, da kuma wani bawan Allah da su dai jami’an suka bindige a Jihar Kano, duk da sunan yaki da fasa-kwaurin shinkafa, wannan kungiya na goyon bayan matakin shari’a da gwamnatocin  Kano da Katsina suka dauka a madadin iyalan wadanda a ka yi wa kisan gillar na bin kadin hakkinsu,” inji kungiyar.

Kungiyar ta kuma sha alwashin cewa ba za ta taba yin kasa-a-gwiwa ba wajen tabbatar da adalci ga duk wanda aka tauye wa hakkinsa.