✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Umma Abdulwahid Dabi: Yadda na yi gwagwarmaya wajen koyarwa

Dokta Umma Abdulwahid Dabi Darakta ce a Jami’ar Arewacin Najeriya da ke garin Kafin Hausa, a Jihar Jigawa. Ta rike mukamin Shugabar Kwalejin Ilimi ta…

Dokta Umma Abdulwahid Dabi Darakta ce a Jami’ar Arewacin Najeriya da ke garin Kafin Hausa, a Jihar Jigawa. Ta rike mukamin Shugabar Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zuba, a Abuja, ta kuma koyar a Jami’ar Abuja da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ta bayyana yadda ta yi gwagwarmaya wajen koyarwa da kuma neman ilimi. Ta bukaci mata su rika neman ilimin addini da na zamani, domin rayuwa ba ta tafiya daidai sai da ilimi.

Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Dokta Umma Abdulwahid, Darakta a Jami’ar Arewacin Najeriya da ke garin Kafin Hausa a Jihar Jigawa. An haife ni a garin Dabi da ke karamar Hukumar Ringim cikin Jihar Jigawa. Dabi tsohon gari ne da yake da dimbin tarihi. Na girma a wurin kanwar mahaifiyata a Kaduna daga shekarar 1967 zuwa 1977. Na yi makarantar sakandire da jami’a a Maiduguri. Na yi karance-karance da dama.
Na fara aiki a Makarantar Koyon Aikin Malunta da ke Kunbotso ta cikin Jihar Kano, daga nan na fara koyarwa a Jami’ar ABU, kafin na koma aiki a Jami’ar Abuja a tsangayar koyar da aikin malunta. Bayan na yi yawo a fagen ilimi sai na dawo jiharmu ta Jigawa don in ba da gudunmuwata. Hakan ya sanya na fara aiki a Jami’ar Arewacin Najeriya da ke garin Kafin Hausa, kuma Alhamdulillahi makarantar tana samun ci gaba da kuma daukaka.
kungiyoyi
Ina cikin harkokin kungiyoyi, musamman wadanda suka shafi taimaka wa mata da kananan yara. Na shiga kungiyoyin mata har ta kai ni ce Shugabar kungiyar daliban Jami’ar Maiduguri, sannan da ni aka kafa kungiyar WRAPA, wato a lokacin da matar Shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubukar take shugabancin kungiyar mata ta kasa. Mu ne muka canji kungiyar Taimaka wa Mata (Family Support Programme) wadda Maryam Abaca ta kafa. Ko a wancan lokacin ma mu ne muka ba da gudunmuwarmu domin ci gaban. Daga nan muka kafa kungiyar USOSA, wato kungiyar Makarantun Hadaka (Unity Schools) da nufin samar da wata mahada domin cim ma wani buri.
Nasarori
Na samu nasarori masu yawa, musamman wajen harkar karatu da koyarwa da ma rayuwar aikin gwamnati. Na rike mukamin shugabar daliban Jami’ar Maiduguri. Na rike mukamin shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zuba a yankin Abuja. na koyar a Jami’ar Abuja da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
kungiyoyi da dama sun ba ni lambar yabo. Na karbi kyaututtuka masu yawa. Na taba samun kyautar girmamawa ta ‘shugaba mafi kwazo’ a lokacin da nake Shugabar Kwalejin Ilimi ta Tarayya.
Burina
Babban burina a rayuwa shi ne, in samu sararin ci gaba da koyarwa a makaranta, kamar yadda nake yi a yanzu. Ina da burin ci gaba da taimaka wa yara, domin ina son ganin matasa sun samu ilimi mai inganci.
Kwalliya
Ni ma’abociyar son kwalliya ce, domin wata mujalla mai suna ‘New Breed’ ta taba buga hotunana. Sun yi hira da ni a kan kwalliya. Sun lura da yadda nake kwalliya ta hanyar daura kallabi salo-salo da kuma yadda nake lullubi da gyale. Bayan sun yi hirar da ni sai suka ce mini ni ce mace mafi inganci wajen kwalliya da suka taba yin hira da ita.
A gaskiya ni mace ce da ba ta son nuna jikinta a fili, saboda ina da burin kare kaina; ina da burin kare mutuncina da na mijina da ’ya’yana da kuma na iyayena. Ina yin kwalliya, amma ba irin ta zamani mai nuna tsiraici ba. Nakan yi mamakin yadda wadansu matan ke daukar kwalliyar da ke nuna sassan jikinsu, hakan ya saba wa addininmu na Musulunci.

Abinci
Abincin da na fi so shi ne, tuwon birabisko da miyar taushe ko da miyar kuka. Ina son taushen kankana. Ban cika son cin  nama ba. Ba ni da ciye-ciye domin ba ni da kwadayi a rayuwata. Ina son tuwon gero da tuwon dawa da danyen nonon shanu. A bangaren ganyayyaki kuma na fi son ganyen zogale da rama da salad da alayyahu, saboda suna kara lafiyar jiki.
Mutanen da ke burge ni
Matan da suka fi burge ni a rayuwata su ne, marigayiya Hajiya Hafsat Ahmadu Bello, matar marigayi Sardauna, saboda kawaicinta. Ita ce mace da ta zabi mutuwarta wajen kare mijinta. Ta tare bakin bindiga a lokacin da aka kai masa hari, ana son a halaka shi, inda aka harbe ta kafin aka kashe hi. Kuma ita ce macen da tafi kowa iya kwalliya, domin ba ta sanya irin wadannan kayan kyale-kyale irin na zamani tun ma a wancan lokacin, sai Magreth Tchatter, saboda ita ce take dafa wa iyalinta abinci duk da mukaminta, wannan halin nata ya burge ni.
Sardauna da Tafawa balewa da Nmandi Azikwe suna burge ni, saboda kishin kasarsu, sun bar mana abubuwan koyi.
Bakin ciki
Abin da ya sanya ni bakin ciki, ya bata mini rai shi ne, yawan mutuwar aure da shaye-shayen matasa da lalacewar tarbiyyar al’umma. Akwai bukatar a nusar da matasa muhimmanci rayuwa. A bangaren ma’aurata kuma akwai rashin hakuri, wanda hakan ke haifar da mace-macen aure, hakan na sanya ni bakin ciki. Akwai bukatar ma’aurata su rika hakuri da juna. Ina  takaicin yadda nake ganin mata kanana amma auren su ya mutu.
Shawara ga mata
Ya kamata iyaye mata su shiga neman ilimin zamani da na addini, kuma su yi hakuri wajen kula da ’ya’yansu mata tare da daidaita zaman ’ya’yansu a gidajen mazajensu, domin kare hakkin aurensu.