✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Lawal Sule Abdullahi: Marubucin da ya fara rubuta littafi tun yana shekara 11 (I)

Ga wadanda suka dade suna cece-kuce da tattaunawa game da shin ko za a iya samun wani dan baiwa mai basira da hazaka tamkar Malam…

Ga wadanda suka dade suna cece-kuce da tattaunawa game da shin ko za a iya samun wani dan baiwa mai basira da hazaka tamkar Malam Abubakar Imam a fagagen da ya yi fice a cikinsu da suka hada da ilmi, aikin gwamnati, fassara, sanin harsuna da kuma rubuce-rubuce? Sai mu ce musu Dokta Lawal Sule Abdullahi, wanda ya fara rubuta littafi tun yana dan shekara 11a duniya, daya ne tamkar da goma a dukkanin fagagen da muka ambata, domin kuwa malami ne shi, dan kasuwa, ma’aikacin gwamnati, masanin harsuna da ya gabatar da mukaloli daban-daban a kusan dukkanin jami’o’i da kwalejojin ilmi da ke jihohin kasar nan da wasu jami’o’in kasashen waje da suka hada da Nahiyar Turai da Asiya da kuma gida Afirka.

A daidai lokacin da ba kowane marubucin labari ne yake iya rubuta wakoki da dukkanin ka’idojinta ba, kamar yadda ba kowane mawaki ne ke iya rubuta labari ba, shi kuwa Dokta Lawal baya ga rubuce-rubucen littattafai a fannoni daban-daban da suka hada da addini, kimiyya da kuma rayuwa a cikin harsunan Hausa da Turanci da kuma Larabci, ya kuma rubuta wakoki cikin wadannan harsuna bila adadin. Kamar yadda ya shaida wa wakilinmu a yayin wata tattaunawa da shi. Daga cikin irin wadannan wakokin har da wata waka mai baiti dari da aka taba kawowa a cikin wannan jarida ta Aminiya mai suna Cukumurdi.

Wane ne Lawal Sule Abdullahi?:

Ga dukkanin masu sauraren shirin Kimiyya a Musulunci a gidan rediyon tarayya da ke Kaduna, sunan Alkali Dokta Lawal Sule Abdullahi ba bako ne ba gare shi.

An haife shi ne a Zariya birnin ilmi, inda ya fara koyon karatu da rubutu a wajen iyayensa da kuma karatun Alkur’ani kafin ya shiga makarantar allo inda ya sauke ya kuma fara hadda yana dan shekara 11.

Daga nan aka sanya shi a makarantar furamare ta Lardi, Arabic School da ke Zariya, inda bayan shekara daya da shigarsa, sanadiyyar horo da imin da ya samu a gaban iyayensa, sai ya dauki jarabawar fita tare da samun nasarar shiga makarantar Horon Malamai na Larabci da ke Katsina (Arabic Teachers College) inda ya kammala a shekarar 1979.

Daga nan bayan shekara daya ya sake yin jarabawar shiga jami’a inda ya yi sa’ar shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ya yi karamar Difiloma a fannin koyarwa inda daga nan ya kuma wucewa Jami’ar Bayero ta Kano ya yi Babbar Difiloma a fannin harsunan larabci da hausa da kuma addinin musulunci (Arabic/Hausa & Islamic Studies).

Ya kara komawa jami’ar Bayero inda ya yi karatun digirinsa na farko a kan harshen larabci da Hausa, daga nan ya tafi hidimar kasa a Jihar Ribas.

Daga nan ya sake dawowa Jami’ar Ahmadu Bello, ya yi digirinsa na biyu a kan harsunan Najeriya da Afrika, sannan har wa yau a wannan jami’ar ta Ahmadu Bello ne ya yi digirinsa na uku, inda ya kai matsayin Dokta, sannan ya halarci kwasa-kwasai daban-daban.

Aikace-aikacensa:

Dakta Lawal Sule Abdullahi, wanda ya gudanar da rayuwarsa tsakanin karatu da aiki, ya yi ayyuka a wurare da dama. Ya fara ne da aikin karantarwa a Gadar Gayan da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, haka ma ya karantar a tsohuwar makarantar nan mai cike da tarihi, wato Kwalejin Alhuda-huda da ke Zariya.

Bayan nan ya yi aiki da Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya da ke Abuja (Federal Capital Territory Administration, FCTA) wacce daga baya ta koma FCDA.

Ya yi aiki da babban kungiyar nan ta Rabidatul Alamil Islamiy (Muslim World League) da cibiyarta ke kasar Saudiyya a sashen bada agaji na musulunci da aka fi sani da (International Islamic Relief Organization) inda suka dauke shi aikin shekara daya, amma saboda kwazonsa suka ci gaba da rike shi har na tsawon shekara biyar a matsayin sakatarensu na Najeriya, inda ya ba shi damar zagaya kusan dukkanin jihohin Najeriya da wasu kasashe.

Bayan nan ya fara aikin alkalanci inda ya zama alkali a karamar kotun musulunci da ke Zariya (Bayan kaddamar da Shari’ar Musulunci Kaduna) daga nan aka tura shi zuwa wani kauye mai suna Aboro da ke Sanga kafin daga baya aka yi masa karin girma tare da canjin wurin aiki zuwa Kaduna daga nan kuma bai dade ba aka tura shi Babban Kotun Shari’a (Upper Shari’a Court) da ke Kachia duka a Jihar Kaduna, inda yake aiki har yanzu a matsayin babban alkali.

Gudummawarsa wajen bunkasa Adabi:

Babu shakka, gudummawar da Dokta Lawal ya bayar wajen bunkasa harshen Hausa da Adabinta ba abin misaltawa ba ne. Baya ga muhadarori da laccoci da ya gabatar a kasashe daban-daban, ya yi rubuce-rubuce da dama kan fannonin da ba kasafai marubutan Hausa suka faye yin rubutu a kai ba. Littattafansa masu suna ‘Wane ne Alkali’ da kuma ‘Kai Wane ne a Kotu?’ misali ne da ke tabbatar da haka, domin kuwa irinsu, idan ma akwai, to kalilan ne cikin harshen Hausa.

A ciki littafinsa ‘Kai Wane ne a kotu’ ya kawo rukunan shari’a ne guda bakwai wadanda shari’a ba ta tsayuwa sai da su. Wadannan rukunai sune; Mai kara, wanda ake kara, shaida, abin da ake jayayya, abin da ake hukunci da shi da kuma tafiyar da shari’a (shafi na 5-7).

Rubuce-rubucensa da suka hada da littattafai da wakoki da kuma kasidun da yake gabatarwa a manyan makarantu sun ginu ne a kan bunkasa harshen hausa da adabinta da kuma wasu fannoni na rayuwa da suka hada da Shari’a da Kimiyya da kuma Rayuwa. 

Zamu ci gaba a mako mai zuwa.