✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokta Amina Aminu dorayi: Mata ku shiga fannin lafiya

Dokta Amina dorayi kwararriyar likita ce .Kuma ita ce karamar mataimakiyar Manaja ta bangaren aikace-aikacen kasa da kasa na kungiyar hadin gwiwa ta kyautata tsarin…

Dokta Amina dorayi kwararriyar likita ce .Kuma ita ce karamar mataimakiyar Manaja ta bangaren aikace-aikacen kasa da kasa na kungiyar hadin gwiwa ta kyautata tsarin harkar lafiya,mataki na biyu.

Dokta Amina dorayi an haife ni a Zariya da ke jihar Kaduna.Na yi makarantar firamare da ke Zariya.Daga nan sai na tafi makarantar ST Luis da ke jihar Kano.Na yi karatun aikin likita a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.Na yi digiri na biyu a fannain kula da lafiyar jama’a a jami’ar Liberpool da ke UK.Na yi wasu karance-karance a sauran makarantu da suka hada da makarantar Habard School of Public Health.Ni ‘yar asalin jihar Kano ce,kuma ni ce karamar mataimakiyar Manaja ta bangaren aikace-aikacen kasa da kasa na kungiyar hadin gwiwa ta kyautata tsarin harkar lafiya,mataki na biyu.

Abin da nake jin dadinsa a aiki
Abin da nake jin dadinsa a aiki a yanzu,shi ne kasancewa ta kwararriyar mai aikin kula da lafiya,domin kuwa ina samun karin ilimi kuma ina zagaya cikin Najeriya domin ziyartar asibitoci masu yawa.A tsarin kula da lafiyar jama’a mun fi kula da hanyoyin kariya daga ciwo a kan bayar da magani.Saboda haka ba a waje daya nake ba ina bayar da magani ,ina zuwa wurare daban-daban da asibitoci domin ganin abubuwan da suke gudana.Kuma ina kula da kasafin kudaden kiwon lafiya tun daga gwamnatin tarayya zuwa jihohi har zuwa kanan hukumomi.Domin idan akwai wadatar kudi mutum zai iya kasancewa cikn koshin lafiya.
kalubale
Akwai kalubale sosai.Kasancewa ta mace ,matar aure kuma ga ‘ya’ya guda uku,sannan ga tafiye-tafiye.Sai da ke nan mutum dole ya bar ‘ya’yansa a hannun kulawar wasu,wannan ba karamin kalubale ne ba.Koda yake duk da haka ina farin ciki domin karamin yarona dan shekara shida ya fahimci ba koda yaushe zai same ni a gida ba.Akwai wani abin sha’awa da ya faru wanda yana daya daga cikin kaluben.daya daga cikin yarana aka ce su rubuta abin da suka lura da shi a wurin daya daga cikin iyayensu.Sai ya yi rubutun a kaina ya ce”Mahaifiyata tana tafiye-tafiye koda yaushe,kuma koda yaushe tana kan waya,sannan duk abin da ake yi a makarantarmu tana zuwa,tana son yin abubuwa da yawa.”Abin ya shige ni domin yana ji A jikinsa cewa mahaifiyarsa ba ta rabuwa da tafiye-tafiye.Duk lokacin da na samu na yi sati biyu a gida ina farin ciki domin na san abu ne mai wuya in yi sati biyu ba tare da na yi tafiya ba.
Burina ina karama
A gaskiya ina karama ba na tunanin zama wani abu.Lokacin ina makarantar sakandire na san ina son Biology da Lissafi da sauran darussa.Ba na sha’awar zama Injiniya domin ina ganin ba zan iya ba.Sai nake sha’awar zama likita kuma abin sha’awa sai ga shi na zama likita ta farko a dangina.Mijina ma likita ne,mahaifiyarsa kuma Nas ce.Ina farin ciki na karanci aikin likita.Dalili shi ne a matsayina na likita ina da zabi masu yawa shi ya sa na zama mai kula da kiwon lafiyar jama’a.Na san ilimina na likita da tafiye-tafiyen da nake yi shi ne ya ba ni damar bayar da gudumawata ga al’umma sosai.A gaskiya zan karfafa wa mata gwiwa domin su shiga fannin lafiya yana da muhimmanci sosai.Kuma duk wani magidanci da yake son matarsa ta taimaka wa al’umma zai yi alfahari cewa matarsa tana taimakawa ta fannin lafiya.
Abubuwan da suke ba ni sha’awa
Suna da yawa ,mu takwas ne,ni ce ta farko.Mun girma aZariya a unguwar da babu hanyoyi masu kyau amma duk da haka koda yaushe muna kan keke muna tukawa,tare da kawayena .Kowa yana da kekensa,kuma akwai zaman lafiya.Amma yanzu ba ma ganin haka,watakila saboda manyan tituna da yawaitar motoci yara ba sa yawo a kan kekuna kamar da.Gaskiya ina tuna wancan lokacin ,kowa abokinka ne, za ka je gidansu ka ci abincin rana ko na dare,amma ka tabbatar ka dawo gida da wuri.Saboda haka ina tuna lokacin kuruciyata tare da kawayena.
Abin da na koya a gurin mahaifiyata
Ban taba ganin mace mai tsafta irin mahaifiyata ba.Ta koya min tsafta sosai,ina ganin duk ta cusa mana wannan dabi’ar.Kuma tsabta ita ce mafi muhimmanci a rayuwa.Sannan kuma kula da ‘ya’ya takwas ba wasa ba ne,amma ta yi shi,kuma har yanzu a tsaye take.Wannan ya sa ina kara ganin girmanta.Ni yanzu ga shi ‘ya’ya uku ne kawai a gabana,amma ina ganin ba zan iya kwatanta abin da ta yi ba ko kusa.Yawanci idan zan yi tafiya nakan bar ’ya’yana a gurinta domin na san za su ci mai kyau su sha mai kyau kuma su yi barcinsu har da minshari.Domin tana da kulawa ta musamman.Mijina ya san ita kadai ce kawai za ta iya kulawa da ‘ya’yana idan na yi tafiya,har ma ta fi ni kula da su.

Lokacin da na zama uwa
Ina da ‘ya mace da kuma maza guda biyu.Lokacin da na haifi ‘yata na yi farin cikin da ban taba yi ba.Ka sani cewa duk dawainiyar yaro tana kanka ba karamin abu ba ne.Abin sha’awa ne ka zama uwa ka raini yaro tare da koya masa tarbiyya.
Yadda na hadu da maigidana
Wannan ita ce shekararmu ta 13 muna zaman aure tare,ina ganin na yi sa’ar miji.Mun hadu da shi a jami’a,ajinmu daya.Na hadu da shi a shekarar 1994,daga baya kuma sai muka yi aure.Abokina ne kuma zai ci gaba da zama abokina.
Mutanen da nake koyi da su
Suna da yawa a ciki da wajen kasar nan.Akwai Margret Thatcher , a cikin kasar nan kuma akwai Hajiya Amina Ibrahim da kuma Oby Ezekwesili da kuma Abike Dabiri Erewa duk wadannan mata ne da suka yi rawar gani ga al’umma.
Kwalliya
Ina son in sake a duk irin kayan da na saka a jikina.Ina son kaya masu saukin sakawa.Ina son kaya masu kyau da sarkokin gwal.Ina so kullum in zauna tsaf.
Inda nake son zuwa hutu
Zan iya cewa Dubai,komai kake so akwai shi a can kamar Disney Land.Ina son Disney Land ma,amma ina son hutu a wurin da zan ga bambanci musamman wurin ruwa.
Abin da nake son a tuna ni da shi
Ina son a tuna da kokarin da nake yi,ina son a tuna ni a matsayin wadda ta taimaka matuka ga rayuwar al’umma musamman mata da ‘yan mata.Ina fita domin koyarwa a makarantun firamare da makarantun sakandare domin ina son gina matasa da mata.Ina so a sanni a matsayin mai inganta rayuwar kowa da kowa.Nakan tattauna da matasa kai tsaye domin su ne manyan gobe,ya kamata a nuna musu su zama nagari domin su zama abin alfahari nan gaba.