Kotu ta sako Dokta Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi, bayan ta tsare shi a gidan gyaran hali.
Fitaccen malamin ya isa gida, inda aka gan shi a majalisinsa, mabiyansa sun shirya masa gagarumar tarba har ya gabatar da jawabi.
Kotun Majistare ta Jihar Bauchi, ta ba da belin Dokta Idris Abdul-aziz ne bayan da kama shi, bisa zargin sa da kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), zargin da ya musanta.
A kan rashin cika sharuddan ne kotu ta ba da umurnin a tisa keyar malamin zuwa gidan gyaran hali
- Barayi 2 da suka sace wayoyin hannu 48 sun shiga hannu a Katsina
- An yi wa tsohuwa mai shekara 80 fyade a Ondo
Kungiyar Fityanul Islam ce dai ta maka malamin a Kotun Majistare da Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.
Kotun ta bayar da belin fitaccen malamin ne bayan bukatar hakan da lauyoyin malamin suka nema.
A ranar Litinin ne, ’yan sanda suka gurfanar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi bisa zargin tayar da hankulan jama’a.
Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda suka gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa kuma tun a makon jiya aka nemi malamin ya amsa goron gayyatar.
’Yan sanda sun gurfanar da malamin ne a Babban Kotun Majistare mai lamba ta 1 kan zargin da ake masa.
alkalin kotun ya hana bayar da beli, sannan ya bayar da umarnin a ajiye wanda ake kara a gidan gyaran hali, tare da bayar da umarin sake dawo da shi gaban kotu ranar Talata.
A watan da ya gabata ma malamin a cikin hudubarsa ta Azumin Ramadana, an zarge shi munana ladabi ga Manzon Allah (SAW).
Sai dai kuma an wasu malaman da suka goyi bayansa da cewa kalamansa na an turba ta gaskiya.
Sai dai a ranar alkalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman na ranar Talata.
Kotun ta bayar da belin malamin ne bisa sharuddain gabatar da wani babban ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi su tsaya masa.
Za kuma su gabatar da takardar mallakar wata kadara da kimarta ta kai Naira miliyan biyar sannan dole ne masu tsaya masa su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu.