Majalisar Karamar Hukumar Sanga da ke jihar Kaduna ta ce, sannu a hankali jama’ar karamar hukumar sun fara sauya tunani ta hanyar kiyaye dokar hana zirga-zirga da sauran harkoki bayan tunda farko wasu sun nuna turjiya.
Yayin da wasu ke zargin gwamnati da cewa wata dabara ce kawai da ta fito da shi don karkatar da kudade daga lalitarta zuwa wani waje na daban.
Shugaban karamar hukumar Misa Charles Danladi, ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a garin Kafanchan a karshen mako.
- Likitoci sun yi watsi da rage albashinsu a Kaduna
- Dagewa da ibada cikin watan Ramadan da kuma bayansa
Mista Danladi, ya ce hakan ya biyo bayan tashi tsaye da majalisar ta yi ne tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen fadakar da jama’a illar annobar ga harkokin lafiya da na tattalin arziki.
Sannan shugaban ya bayyana takaicinsa kan manyan motocin da ba su dauke da kayayyakin da aka yarda su wuce suke dakile kokarin da gwamnatin karamar hukumar ke yi wajen tabbatar da dokar hana zirga-zirgar inda ya ce hakan, babbar barazana ce ga jama’ar yankin.
Bayan yabawa jama’ar yankin da ya yi a karshe, shugaban ya kuma yi kira a gare su da su rika lura da sa ido tare da kai rahoton duk wani matafiyi, bako ko dan gari da ya sulalo zuwa karamar hukumar daga wani waje musamman wuraren da cutar COVID-19 tayi kamari, domin a killace shi don tabbatar da ba shi dauke da kwayar cutar.