Mutum 875 ne aka kai rahoton sun kashe kansu bayan da aka ayyana dokar kulle a kasar Nepal.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun 24 ga watan Maris al’ummar kasar ta Nepal ke zaman gida bayan kafa dokar da nufin hana yaduwar coronavirus.
Wasu alkaluma da ‘yan sandan Nepal suka fitar sun nuna cewa yawan mutanen da suka kashe kansu a fadin kasar ya karu da kashi 16 cikin 100 a wata na farko na dokar.
Daga tsakiyar watan Maris zuwa tsakiyar watan Afrilu an kai rahoton mutanen da suka kashe kansu har 482 a ofisoshin ‘yan sanda da ke fadin kasar, sabanin 414 da aka samu daga tsakiyar watan Fabrairu zuwa tsakiyar watan Maris.
Wadannan alkaluma na nuna cewa adadin wadanda suka kashe kansu a lokacin dokar ya yi sama kasasncewar a yankin Kathmandu (babban birnin kasar) da kewaye kawai mutum 38 ne suka kashe kansu.
- Kasashen da Coronavirus ba ta hallaka kowa ba
- Yaki da Coronavirus: China za ta ba da dala biliyan biyu
‘Matsalar Kwakwalwa ce’
Galibin wadanda suka kashe kan nasu dai, wato 742, sun rataye kansu ne, yayin da 114 suka sha guba.
Sauran kuma sun hallaka kansu ne ta hanyar cinna wa kansu wuta, ko caka wuka, ko durowa daga sama.
“An tattara wadannan alkaluma ne zuwa ranar 16 ga watan Mayu”, inji Niraj Bahadur Shahi, kakakin rundunar ‘yan sandan, wanda ya kara da cewa an ci gaba da tattara alklauma bayan nan.
Masana da dama dai sun alakanta kashe-kashen da lafiyar kwakwalwar mutanen da lamarin ya shafa, wadanda aka tilastawa zaman gida a karkashin dokar.