✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar kiwon shanu a Ekiti:Fulani na cikin tsaka mai wuya

A ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya rattaba hannu a sabuwar  dokar kiwon shanu ta jihar a sa’ilin…

A ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya rattaba hannu a sabuwar  dokar kiwon shanu ta jihar a sa’ilin da ya yi wata ganawa da sarakunan gargajiyar jihar su kimanin 3000.
Dokar da gwamnan ya rattaba wa hannu ta haramta wa  makiyaya  kiwo da makami da kiwo a wuraren da ba a tanada   domin yin kiwo ba, za kuma a daure  duk makiyayin da ya saki dabobbinsa suka yi kiwo a wuraren da ba a tanada  domin yin kiwo ba daurin wattani shida ba tare da zabin tara ba.  Kana za a tuhumi duk makiyayin da aka samu yana kiwo dauke da makami da laifin ta’addanci.
A martanin da ya yi bisa wannan doka, Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta miyyati Allah a Jihar Ekiti, Alhaji Muhammadu Nasamu ya shaida wa Aminiya cewa, Gwamna Fayose bai yi musu adalci a dokar da ya rattaba wa hannu ba. Domin bai gayyaci shugabannin Fulani makiyaya a taron da ya yi ba.
 “Ta yaya za ka yi doka a kan al’umma ba tare da ka tuntube su ba? Ka ga mu a kafafen yada labarai muka tsinci batun, ba a yi damu ba. Ai  ka ga babu adalci ke nan, na ji wai an hana yin tafiya da shanu da daddare ai ka ga in haka ne wannan abu ne mai wuya,  domin babu hanyar shanu ko daya a Jihar Ekiti, to idan da rana za ka kora shanun ka abin ba zai yiwu ba, saboda cunkoson jama’a da ababen hawa. Sannan  in ka lura duk Bafulatanin da zai koro shanunsa daga Arewa ya yiwo Kurmi da su, dole ne ya ratso ta Jihar Ekiti, to ya ake so mu yi ke nan? Mu dai a ganinmu shi gwamnan yana so ne ya huce adawar siyasarsa da Shugaba Buhari a kan Fulani makiyaya, don haka muke kai kukan mu ga gwamnatin tarayya da ta dube mu da idon rahama “ inji shi .
Sakataren kungiyar ta Miyyetti Allah a Jihar Ekiti Malam Zayyanu Muhammad  ya shaida wa Aminiya cewa,  Fulani makiyaya na cikin halin tsaka mai wuya a jihar, domin abin bai tsaya ga dokar da gwamna ya rattaba wa hanu kawai ba, hatta mutanen gari na amfani da wannan damar wajen muzguna musu.
 “Ni abin da ya fi ba ni haushi ma abin har da jami’an ‘yan sanda. Domin a makon nan ne wata saniyar mu ta yi sabuwar haihuwa, sai aka fita kiwo da ita aka bar dan nata a gida. To kasan halin dabba ba tare da an lura ba sai ta sulale ta koma gida ta taho da dan ta sake yunkurin komawa wajen kiwo; daga nan ta saki hanya ta yiwo kan titi,  nan take DPO ‘yan sandan yankin Ologede ya sa aka kama saniyar. Nan fa  muka yi ta fama, inda ya ce mana daman gwamna ya ce ba ya son saniya. Don haka shi harbeta ma zai yi sai da muka ba shi Naira dubu 10, sannan muka karbi saniyar, ai ka ga ya za a yi a ce jami’an tsaro na gwamnatin tarayya yana barazanar harbe dabba” inji shi.
Zayyanu Muhammad ya kara da cewa, maganar kiwo da makami ma daman ba ta taso ba. Domin babu gaskiya a maganar da ake yi wai Fulani na yin kiwo da manyan makamai kamar su bindigogin AK47
“Wannan babu kamshin gaskiya, duk Bafulatanin da ka gani da bindigar AK47 ya tashi daga makiyayi ya koma dan fashi da makami, domin duk makiyayin arziki makamin da yake kiwo da shi, shi ne sandar da yake kora dabbarsa, sai adda da yake rikewa domin amfanin kansa da dabbar. Kuma kadan daga ciki shi ne in dabbarsa ta kasa sai ya yanka ya kira mahauci ya saya. Haka in ya shiga surkuki dabbar ta gaza fita sai ya sassare reshen icce ya yi mata hanya, sannan in ya gamu da mugun kwaro irin su maciji ko makamancin haka ya kasha. Wannan shi ne dalilin kiwo da sanda ko  adda,” inji shi.
Jami’in tsare-tsare na kungiyar manoma ta kasa reshan Jihar Ekiti Mista Adeleye Kolade  ya shaida wa Aminiya cewa, manoman jihar sun yi lale da marhabin da wannan doka da ‘yan majalisar jihar suka yi Gwamna Fayose ya rattaba wa hannu.
Ya ce dokar na cikin sharuddan da kungiyarsu ta cimma, tare da ta Fulani makiyaya a taron da suka yi, wanda kwamishinan noma na jihar ya jagoranta a fadar babban Basaraken jihar wato Ewi na Ado Ekiti, taron da ya gudana a ƙarshen shekarar da ta gabata ya kuma sami halarcin shugaban ƙungiyar miyyati Allah na ƙasa Alhaji Muhammdu Kirwa wanda ya jagoranci shuwagabbanin fulani ya kuma yiwa mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar wakilci. Mista Kolade yayi kira ga shugaba Buhari ya bai wa dokar goyon baya domin ci gaban manoma da makiyayan jihar baki daya.