Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce dokar kayyade shekarun aure ga ’yan mata zuwa shekara 18 wani yunkuri ne na yin karan-tsaye ga Musulunci da kuma takalar Musulmi domin a kuntata musu.
Sheikh dahiru Bauchi ya bayyana haka ne ga manema labarai a Bauchi a karshen makon jiya, inda ya shawarci ’yan Majalisar Dattawa da ta Tarayya su rika lura da dokokin da za su haifar da ci gaba tsakanin jama’a maimakon zaunawa suna bata lokaci kan maganganun da ake taso da su domin karkata hankulan mutane zuwa ga abin da ba shi ne damuwarsu ba.
Ya ce abokan gabar Musulunci ke kawo rudani don raba kan mutane da kuma shiga gonar Allah tare da saba maSa, don haka ya shawarci masu fada a ji a kasar nan su koma ga Allah su samar da abin da zai ciyar da kasa da mutanenta gaba.
Sheikh dahiru Bauchi ya ce Musulmin Najeriya duk abin da Allah da ManzonSa suka ce a yi shi suke yi, ba sa bukatar shigar da mutane hanyar saba wa Allah da ManzonSa, saboda Allah da ManzonSa sun fi kowa ilimi da tausayi da sanin ya kamata da sanin abin da ya fi dacewa da dan Adam.
Ya ce akwai dokokin ’yancin dan Adam da na addini a dokokin duniya da hatta Nasara ya yarda da su, don haka Musulunci ne ya tsara rayuwar da ake mutunta mutane da addininsu, don haka dokar ba ta dace da Musulunci da Musulmi ba, saboda Manzon Allah (SAW) ya auri A’isha tana da shekara shida ta tare da shekara tara.
Game da batun auren jinsi kuwa Shehin ya ce wani abu ne da kafirai ke fito da shi don cin zarafin Musulmi da sauran masu addini. Ya ce kowa ya san idan da mace za ta auri mace ko namiji ya auri namiji duniya za ta kare. Ya ce sai idan mace ta auri namiji, namiji ya auri mace ne kurum za a samu ci gaban rayuwa ta hanyar haihuwa.
Shehin ya ce hatta dabbobi ba a ganin namiji na bin namiji ko mace na bin mace, don haka ya gargadi ’yan majalisa su daina biye irin wadannan maganganu da ka iya tayar da rudani ko saukar da bala’i a cikin kasa.
Dokar kayyade shekarun aure takalar Musulmi ne – Sheikh dahiru Bauchi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce dokar kayyade shekarun aure ga ’yan mata zuwa shekara 18 wani yunkuri ne na…
