Babu wata jiha a fadin Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta bai wa izinin samar wa kungiyar tsaronta makami, a cewar Fadar Shugaban Kasa.
Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa umarnin da Shugaba Buhari da ta haramta rike bindiga kirar AK-47 na nan daram, kuma dole ne duk wanda ya mallake ta ya mika ta ga hukumomin tsaro.
- An kaddamar da kungiyar tsaro a Adamawa don magance rikicin manoma da makiyaya
- Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar tsaron Amotekun
“Wanda duk ya ki ya mika irin wannan makamin, an ba jami’an tsaro damar hukunta shi a matsayin dan ta’adda,” in ji Garba Shehu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro ne ke da alhakkin bayar da izinin mallakar makami ga duk wata kungiya, tare da amincewar shugaban kasa.
Ya kara cewa ya zuwa yanzu babu wata jiha a fadin Najeriya da aka bai wa wannan izini.
Wannan sanarwar gargadin na zuwa ne bayan da Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya soki Gwamnatin Tarayya kan hana shi bai wa kungiyar tsaro ta Amotekun makami, alhali ta kyale takwarar Amotekun a Jihar Katsina izinin mallakar makami.