An raba buhun shinkafa 1,200 ga mutanen Daura, inda gwamnatin jihar Katsina ta ayyana dokar hana fita ta tsawon mako biyu.
Shugaban riko na karamar hukumar Daura, Alhaji Hussaini Rafindadi, wanda ya karbi tireloli biyu na shinkafar ya ce an yi rabo na Allah da Annabi.
“An raba wadannan buhunan shinkafa kamar yadda ya dace; an ba ko wacce rumfar zabe buhu shida.
“Muna da rumfunan zabe 171 a karamar hukumar, in aka lissafa za’a ga an bayar da buhu 1,026 daga cikin 1,200.
“Sauran da suka rage, an baiwa kungiyar nakasassu da ta Kiristocin da ke zaune a yankin tare kuma da su ‘yan kwamitin da suka aiwatar da wannan aiki”, inji Alhaji Hussaini.
Gwamnatin jihar ce dai bayar da gudunmawar shinkafar domin a rarraba wa masu karamin karfi da nakasassu domin rage radadin da suke fuskanta sakamkon rufe karamar hukumar da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.
- COVID-19: An kafa dokar hana fita a Daura
- Coronavirus: Abubuwa sun daidaita a Daura
- COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai
Kafin bai wa ‘yan kwamitin rabon buhunan shinkafar, sai da Alhaji Hussaini ya gargade su da su ji tsoron Allah a wajen gudanar da wannan aiki mai nauyi da ya rataya a kan su.
Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar ta Daura, Alhaji Nasiru Yahaya, ya ja hankalin al’ummar yankin da su ci gaba da hakuri a kan wannan jarabawa da Allah ya nufe su da ita, sannan su ci gaba da kiyaye doka tare da kiyaye dukkan sharuddan da aka gindaya domin hana ci gaba da yaduwar wannan cuta.
Wata uwa mai suna Murja Ibrahim da ta samu tallafin ta ce ta ji dadin tallafin.
“Kullum sai mun fita don nemowa, to kuma sai ga wannan lalura da ta same mu. To wannan tallafi gaskiya ya taimaka mana sosai, ba ma kamar gare mu iyaye mata da ke da marayu”, inji Malama Murja.
Shi kuwa Ali Sani cewa ya yi, “Muna jin labarin yadda wasu jihohin suke yi, amma gaskiya…wannan tallafi ya zo mana ba tare da mun yi zato ba”.
Daura ce karamar hukuma ta farko da aka ayyana dokar hana fita a jihar Katsina, bayan da aka tabbatar samun wanda ya kamu da cutar coronavirus.