✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji

 Dogo Gide ga Zamfarawa: Ku tsaya ku yi noma abinku  A ranar Larabar makon jiya ne aka fara samun labaran da suke nuna cewa wani…

 Dogo Gide ga Zamfarawa: Ku tsaya ku yi noma abinku 

A ranar Larabar makon jiya ne aka fara samun labaran da suke nuna cewa wani mai suna Dogo Gide ya hallaka fitaccen barawon shanun nan kuma dan fashi da ke yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a Jihar Zamfara wato Buhari Tsoho, da aka fi sani da Janar Buharin Daji.

Bayanai sun ce Dogo Gide yana daya daga cikin abokan ta’addancin marigayi Buharin Daji wadanda suka tuba tare a bara, kafin Buharin Dajin ya koma ruwa.

Bayanan da Aminiya ta samu sun ce Dogo Gide mutumin gundumar dansadau ne kamar Buharin Dajin wanda ya fito daga kauyen dangulbi da ke kusa da dansadau, sai dai dukan wadanda Aminiya ta tuntuba sun ce ba za su iya cewa ga takamaiman garin su Dogo Gide ba, kasancewarsa Bafulatani makiyayi da yake yawo da shanu har zuwa wasu jihohin kasar nan.

Majiyoyinmu sun ce Dogo Gide matashi ne kuma yana da mace har da ’ya’ya. Sai dai wata majiya ta ce Dogo Gide ya taba kasancewa mataimakin Buharin Daji kafin su raba gari.

Wani wanda bai son a ambaci sunansa kuma wanda ya san wani abu game da Dogo Gide ya shaida wa Aminya cewa “Dogo Gide matashi ne da shekarunsa ba su wuce arba’in ba.” Kuma ya tabbatar da cewa a baya Dogo Gide ya kasance a cikin kungiyar barayin shanun kuma yana daga cikin wadanda suke cin karensu ba babbaka tare da yaran Buharin Daji. Ya kara da cewa hasali ma an ce Dogo Gide yaron Buharin Daji ne. 

Ya ce “kungiyar barayin shanun tana da wata ka’ida, kuma ka’idar ita ce idan ba ka son shiga cikin kungiyar tasu alhali kai Bafulatani ne, to dole ne wani a cikin iyalanku ya kasance a cikin kungiyar.”

“Kasancewar daya daga cikin iyalanku mamba a kungiyar zai sa dukiyarku ta shanu ta tsira daga sata. Shi ne dalilin da ya sa za a ga wadansu Fulani suna zama cikin daji da shanunsu amma sun tsira daga hare-hare,” inji shi 

Ya kara da cewa, “Babban dalilin da ya sa Dogo Gide ya kashe Buharin Daji shi ne, shi Dogo Gide ya bar harkar satar shanu. Kuma kamar ya yanke mu’amala da Buharin Daji da yaransa, to sai Buharin Daji ya tura yaransa suka je suka sato shanun surukan Dogo Giden har suka kashe wadansu daga cikin iyalan gidan.”

Ya ce wannan ne ake jin dalilin da ya sa Dogo Gide ya shirya yadda zai hallaka Buharin Daji kuma ya samu nasara.

Ya ce wasu rahotanni sun ce bayan Dogo Gide ya tuba daga satar shanun ya dawo yana taimaka wa jami’an tsaro da bayannan sirri. Amma huldarsa da jimi’an tsaron ba ta kai-tsaye ba ce, yana huldar da su ne ta hannun wadansu ’yan sa-kai. 

Ya ce ko lokacin da aka je dauko gawar Buharin Dajin ma, sai da Dogo Gide ya tura yaransa biyu suka nuna wa jami’an tsaro gawar kafin su dauko ta. 


Gide ga Zamfarwa: Ku 

tsaya ku yi noma abinku

Hankalin mazauna kauyukan Jihar Zamfara ya fara kwantawa bayan hallaka gawurtaccen dan fashin nan kuma barawon shanun da ake kira Buharin Daji, wanda ya addabi jihar.

Buhari Tsoho wanda aka fi sani da Janar Buharin Daji shi da ’ya’yan kungiyarsa ta barayin shanu sun dade suna cin karensu babu babbaka a cikin dazukan Jihar Zamfara da makwabtanta.

Aminiya ta samu labarin cewa Dogo Gide ya fada wa wadansu mazauna kauyukan Zamfara da suka fi fama da hare-haren ’yan bindigar cewa kada su razana ba za su kai musu hari ba.

Wani mazaunin yankin mai suna Ali Hassan ya shaida wa wakilinmu cewa Dogo Gide ya shaida wa mazauna kauyukan Madaka da Gajeren kauye da kuma Karauchi da ke Gundumar dansadau cewa kada su razana shi ba zai kashe su ba.

“Lokacin da mazauna kauyukan suka hango Dogo Gide da yaransa sai suka tsorata suka fara guduwa, saboda suna tsammanin yaran Buharin Daji ne, domin sukan wuce ta wuraren. Amma da ya zo kusa da su sai ya fada masu cewa shi ne Dogo Gide, kuma su daina gudu, su tsaya su yi noma domin za a samu zaman lafiya,” inji shi.

Shi ma wani daga garin Mutunji mai suna Garba Shawai ya fada wa Aminiya cewa yanzu hankalinsu ya fara kwanciya kuma sun yi wa Allah godiya a kan nasarar da aka samu ta kashe jagoran ’yan ina-da-kisa na yankin. “Mun yi matukar shan wahala, an hana mu noma da kiwo, ni kaina na yi asarar shanu sama da 300. Kuma yaran Buharin Daji ne suka dauke shanun baya ga kashe mini ’ya’ya da suka yi,” inji shi.

Shi kuwa Tanimu Malau, cewa ya yi babu abin da yake tayar musu hankali game da Buharin Daji illa kisan jama’a babu gaira babu dalili. Ya ce shi da mutanensa sukan zo kauye su kashe mutane su kone rumbunan abinci su yi tafiyarsu. “A da har mun fitar da ran cewa za a kawo karshen matsalar nan, amma yanzu muna ji a jikinmu cewa al’amura za su gyaru, zaman lafiya zai dawo kamar da,” inji shi.

Haka shi ma Isah Abari ya ce a kowane irin yaki aka kashe shugaba, to an gama cin abokan gaba da yaki, kuma dole ne su yi saranda. “Kamata ya yi yaran Buharin Daji idan ma akawai sauransu, to su mika wuya su rungumi zaman lafiya. Kuma ya kamata mutuwar shugabansu ta zama darasi a gare su,” inji shi.


Yadda ajalin Buhari Daji 

ya zo karshe

 A kwanakin baya wani sakon murya da aka rika yadawa ta waya wanda aka tabbatar Buharin Daji ne yake magana da wani a Jihar ta Zamfara ya rika yawo a kafar sada zumunta, inda a ciki aka ji Buharin Dajin yana cewa sai Maiduguri ta fi Jihar Zamfara kwanciyar hankali muddin ba a saki wani na hannun damarsa da ake kira Dogon Bangaje da ’ya’yansa da matarsa da Hukumar DSS ta kama ba.

An kuma ji shi yana cewa noma ba zai yiwu a JiharZamfara ba kuma duk hare-haren da ake kaiwa ga kauyukan jihar yanzu za a kai wadanda suka fi na baya muni.

Sai dai kwatsam a ranar Larabar makon jiya ana cikin tashin hankalin jin irin wadanan maganganu ne sai aka ji labarin cewa wani tsohon yaronsa da ake kira Dogo Gide ya kashe shi bayan wata takaddama a tsakaninsu. 

Dogo Gide dai ya kasance yaron Buharin Daji ne amma ya tuba ya daina harkar satar shanu da fashi a wani zaman sulhu da gwamnati ta yi da su tare da shi kansa Buharin Dajin, wanda ya amince ya ajiye makamansa, ya kuma rungumi zaman lafiya, to amma daga baya Buharin Dajin ya karya alkawarin da ya dauka na dakatar da hare-haren.

Rohotanni sun ce Dogo Gide wanda ake kyautata zaton yana taimaka wa hukumomin tsaro ya fusata da Buharin Daji ne bayan da yaran Buharin suka je suka sace shannun surukansa kuma suka kashe biyu daga cikin iyalansu.

Majiyarmu ta ce Dogo Gide ya je wurin Buharin Daji ya bukaci ya ba da shanun da yaransa suka kore a gidan surukansa. Amma sai Buharin Dajin ya ki sakin shanun, har ma ya fada wa Dogo cewa yaransa sun riga sun raba shanun a tsakaninsu.

Wannan inji majiyarmu ya fusata Dogo Gide ya kuduri aniyar kashe Buharin Daji da wadansu daga cikin yaransa, inda ya yi amfani da kiran taron yadda za a sulhunta tsakaninsu ya dirka wa Buharin Daji bindiga ya fadi ya mutu.

Majiyarmu ta ce hakan na faruwa sai fada ya kaure a tsakanin bangaren Dogo Gide da kuma yaran Buharin Daji, inda su Dogo Gide suka yi nasarar hallaka Buharin Daji da yaransa takwas.

Wadansu da suka san yadda lamarin ya auku sun shaida wa wakilinmu cewa yaran Buharin Daji sun yi ta yin kokarin zuwa su dauke gawarsa su tafi da ita, amma su Dogo Gide suka hana su ta hanyar kai musu hari da bindigogi.

Wani mazaunin yankin ya ce wani jami’in tsaro ya shaida musu cewa sun ga kasusuwan gawarwakin mutanen da ake zaton na wadanda Buharin Daji ya kashe ne a cikin dajin.

A watan Fabrairun bara ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta kulla yarjejeniya da Buharin Daji, domin samar da zaman lafiya a jihar, amma ba a daina kashe-kashen mutane a jihar ba.

Ko a watan jiya ’yan bindiga sun kashe mutum 35 a harin da suka kai kauyen Birane da ke karamar Hukumar Zurmi da ke jihar.


An kashe daruruwan 

mutane a shekara 7

daruruwan mutane ne kungiyar su Buharin daji suka kashe a cikin shekara bakwai da suka wuce, kuma an zarge su Buharin Dajin da yi wa mata da yawa fyade baya ga sace jama’a suna neman kudin fansa. 

A watan jiya daya daga cikin ’yan Majalisar Dattawan da suka fito daga jihar Sanata Kabiru Marafa, ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1,400 a sassan jihar cikin shekara biyar.

An kai wani rukunin sojoji na musamman da ake kira da Operation Harbin Kunama zuwa Zamfara domin yaki da barayin shanu da ’yan fashin, amma duk da haka aka ci gaba kashe mutane.

Sai dai a yayin da labarin kashe Buharin Daji ya faranta wa mutane da dama rai jihar, da sauran makwabtanta ba a sani ba ko hakan zai dawo da dauwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara da mkwabtanta.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto an ajiye gawar Buharin Daji a Cibiyar Kiwon Lafita ta Tarayya da ke Gusau, kuma hukumomin jihar sun ce nan gaba za su ba da sanarwar mataki na gaba da za su dauka.