✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogara ya kafa kwamiti don binciken badakalar dawo da Maina

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya kafa kwamitin da zai binciki dawo da tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa kan garambawul din fansho, Abdulrasheed Maina. Kwamitin…

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya kafa kwamitin da zai binciki dawo da tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa kan garambawul din fansho, Abdulrasheed Maina.
Kwamitin wanda ya kunshi membobi 10 da Dan majalisa Aliyu Sani Madaki daga jam’iyyar APC daga jihar Kano ke yi wa jagoranci ya hada da Jagaba Adam da Abubakar Danburam Nuhu da Ayo Omidiran da Solomon Adeolu da Kinsley Chinda da Yunusa Abubakar da Timothy Golu da Kehinde Odeneye da Olusegun da kuma Sergius Oseasochie Ogun.
Kafa kwamitin da zai binciki bacewa da bayyana tare da mayar da Maina aiki ya biyo bayan amincewar da ’yan majalisar suka yi a makon da ya gabata bayan kudurin da Jagaba ya gabatar a zauren majalisar.