Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukkan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.” Karin Magana 3:5-6
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka. Barkanmu da sake saduwa don ci gaba da nazari a kan Ubangiji ne madogararmu.
A kowace rana mukan yi shirye-shiryen harkokinmu na yau da kullum, wadansu ma ba sa iya yin barci sai sun ga cewa sun lissafa, sun kuma shirya harkokinsu na gobe. Yin shiri na da kyau kwarai da gaske amma idan fa muka sa komai cikin hannun Ubangiji Allah muka kuma dogara gare Shi cewa da ikonSa ne za mu ci nasara cikin shirye-shiryenmu.
Karin Magana 16:1-3, Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce. Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji Yana auna manufarka. Ka roki Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.
Duk shirin da mutum ke yi ba tare da nufin Ubangiji ba, to, wannan duk a banza ne dalili kuwa shi ne ba mu san abin da zai faru a yanzu ko da jimawa ba, Ubangiji kadai ke da ikon sanin wannan. Shi ya sa yana da muhimmanci kwarai da gaske mu nemi nufinSa da jagorancin Ubangiji cikin rayuwanrmu a koyaushe.
Bari mu ga misali da wani mai arziki da Yesu Almasihu ya bayar cikin Littafin Luka 12:16-21, Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka kwarai. Sai ya ce a ransa, ‘To, kaka zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina wasu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. Zan kuma ce wa raina, “Lallai ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagalina.” Amma Allah Ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karbi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’ Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba ya kuwa da wani tanadi a gun Allah.”
Haka rayuwar mutane da dama take a yau, mukan kwallafa ranmu ga tattalinmu ko mu ce arzikin da muke da shi, shin, wa ke ba da arzikin? Wa kuma ke da ikon karba? Idan haka ne, me zai hana mu neman wanda ke da ikon tanadawa ya kuma karbe cikin kibtawar ido?
Kariya fa? Mun ga wadansu da sukan gina kariya kewaye da su, za ka gansu tafe da sojoji, ko ’yan sanda da motoci masu sulke, duk wannan na nufin ba wanda zai iya taba rayuwarsu. Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ke fadi game da irin wadannan mutane.
Irmiya 17:5-8, Ubangiji Ya ce: “La’ananne ne mutumin da ke dogara ga mutum, Wanda jiki ne makaminsa, Wanda ya juya wa Ubangiji baya, Gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A kasar gishiri, inda ba kowa. “Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa. Shi kamar itace ne wanda aka dasa a bakin rafi, Wanda ke mika saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin ’ya’ya ba.”
Zabura 20:7-8, Wadansu ga karusan yakinsu suke dogara, Wadansu kuwa ga dawakansu, Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara! Za su yi tuntube su fādi, Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!”
To ka ji, dogara ga karfi ko kariyar kanmu ba za su hana mutuwa ko asara ba, bari madogararmu ta zamana cikin Ubangiji da ke da iko bisa komai, gama zai aiko da mala’ikunSa su kare ka daga kowane irin bala’i.
Za mu rufe da Zabura 62:5-12:
“Ga Allah kadai na dogara, A gare Shi na sa zuciyata. Shi kadai ne Mai kiyaye ni, Mai cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam. Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne kakkarfan makiyayina, Shi ne mafakata. Ya jama’ata, ku dogara ga Allah a kowane lokaci! Ku fada maSa dukan wahalarku, Gama Shi ne mafakarmu. Talakawa kamar shakar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma’auni, sam ba su da nauyin komai, Sun fi numfashi shakaf. Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar komai ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta karu, Kada ku dogara gare ta. Sau daya Allah Ya fada, Sau biyu na ji, cewa Allah Yake da iko. Madawwamiyar kauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji! Kake saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa.”
Shalom!