✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dodo Fura

Wani saurayi ne a karkara, ya kai ziyara zuwa gidan surukansa, sai aka kawo masa fura damamma, ta sha nono sosai, amma saboda kunya sai…

Wani saurayi ne a karkara, ya kai ziyara zuwa gidan surukansa, sai aka kawo masa fura damamma, ta sha nono sosai, amma saboda kunya sai ya ce ya koshi. Wani abin mamaki, a ransa kuma yana matukar kwadayin furar nan. Maimakon a mayar da kokon furar, sai aka ajiye a gabansa, kuma daidai lokacin sai aka dauke wuta. Shi kuwa sai ya dauki kokon ya kai bakinsa, kafin ma ya kurba sai aka dawo da wuta, haske ya baibaye ko’ina. Saboda kunya, sai ya kwarara furar a fuskarsa ya ce wa surukarsa: “Zan miki dodon fura!”
Daga A’isha Ingawa 08163814771