Kwana guda bayan zargin soja da harbe wani direban tanka a hanyar Zariya zuwa Kano, direbobin tanka sun rufe hanyar don gudanar da zanga-zanga.
Da misalin karfe 3:30 na ranar Laraba ne dai wani soja da ke aiki a wani kamfanin gini ya harbe direban har lahira bayan sun samu sabani a Tashar Yari da ke Makarfi, kusa da babbar hanyar.
Duk kokarin da ’yan sanda da Kungiyar Ma’aikatan Sufuri (NURTW) na bude hanyar tun a ranar Laraba ya ci tura, direbobin tankar sun ki janye motocinsu.
Kwamandan Hukumar kiyaye Haddura na shiyyar, Lawal Garba, ya ce duk da ba su gano musabbabin zanga-zangar ba, bincikensu ya tabbatar da an harbe direban tankar.
“Wannan lamari dai bai yi dadi ba, domin tun ranar Laraba abu ya ki ci, ya ki cinyewa; mutane na shan wahala sakamakon hakan”, a cewarsa.
Sai dai ya ce hukumar na ci gaba da kokarin shawo kan lamarin, da taimakon sauran masu ruwa da tsaki.