Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar da wani direban babbar mota ya murkushe wata tsohuwa mai shekara 73 mai suna Titilayo Adawi a jihar.
Matar ta gamu da ajalinta ne a hanyar Lekki zuwa Epe da ke jihar, kuma nan take ta ce ga garinku nan.
- Wike ya ba PDP gudunmawar motoci 25 a Binuwai
- Zargin sakin tsohon Kwamishinan da ya ‘kashe’ abokinsa ya jawo zanga-zanga a Bauchi
Kakakin rundunar a jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), faruwar lamarin a ranar Talata.
Hundeyin ya ce hatsarin ya auku ne a ranar Litinin kuma an kai rahotonsa ga ofishinsu na Ilasan da misalin karfe 12:10 na rana.
Ya ce rahoton da baturen ’yan sanda (DPO) ya samu ya nuna wata mota kirar TATA Lorry mai lamba KRD-165-XZ, wanda wani Kazeem Ajibola ke tuka matar, wanda aka yi zargin shi ne ya murkushe matar.
Wani ganau ya shaida cewar hatsarin ya faru ne a madakar mota ta Salem, a kan hanyar Lekki zuwa Epe, a Victoria Island, Jihar Legas.
“Sakamakon hatsarin, wadda abin ya shafa ta mutu nan take. A bisa rahoton, tawagar jami’an ababen hawa da suka ziyarci wurin sun dauki hotunan abubuwan da suka faru.
“Sun dauke gawar tare da ajiye ta a dakin ajiyar gawa don gudanar da bincike .
“A halin da ake ciki, an kama direban kuma an kai motar zuwa ofishin binciken ababen hawa,” inji shi.
Hundeyin ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.