✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direba da ustaz

Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan…

Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan an cika mota da fasinja sai ustaz ya ce su kawo kudin mota. Da aka fara bashi kudin, sai ya shafa aljihu domin ya ba wani mutum canji sai ya ji babu kudin da suka yini suna aiki a aljihun, wani ya sace. Nan da nan sai ya fara kabbara da karfi, ya ce: “Allahu akbar, wani ya cuci kansa!” Direba ya juyo ya ce: “Ustaz, yaya aka yi ne?” Shi kuwa ya ce: “Ai duk cinikin da muka yi yau, wani ya sace su.” Direba ya ce: “Ka ce ya cuci kansa ko dai ya cuce mu?”
Daga Khalil Muhammad, 08031908918