Duk da samamen da jami’an ‘yan sanda suka kai gidan Sanata Dino Melaye, ba zai hana ci gaba da bincikensa ba har sai ya mika wuya ga hukumar ‘yan sandan Najeriya wajen binciken da take yi masa.
Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ‘yan sandan Najeriya DCP Jimoh Moshood na cewa, ana neman Sanata Dino don tuhumarsa akan wasu laifuka da ke da alaka yunkurin kisan kai a ranar 19 ga watan Yuli 2018.
Moshood ya kara da cewa, Sanata Dino tare da ‘yan daba sun kaiwa Jami’an ‘yan sanda hari inda suka yi harbi da bindiga suka jikkata Sajen Danjuma Saliu wanda ke cikin mobayil na 37 da ke binciken motoci a hanyar Mopa a unguwar Aiyetoro Gbede jihar Kogi.