Tun ina karami na dauki karya a matsayin wata aba mai zubar da kima da mutuncin ko ma waye a idon wanda ake yi wa.
Yawancin lokaci idan babana zai fita aikin kanikancinsa, ina ba shi sallahun sawo min alawa ko biskit.
Idan ya dawo hannu-rabbana, sai na ji ba dadi, har dai na fitar da tsammani na rika yi masa kallon mai zuki-ta-malli a dukkan alkawuran da yake min.
Ba mu shaku sosai ba, domin kuwa lokacin da suka rabu da Innata ban yi wayo ba.
Muka koma wani gida tare da kanwata, inda Inna ke yin ’yan kananan sana’o’in dogaro da kai.
Lokacin ina firamare aji biyu ko uku mahaifina ya bar duniya. Ya bar ’ya’ya da dama, kowanne mahaifiyarsa daban.
Na kammala sakandare a daddafe, sannan na shiga fafutukar yau da gobe.
Na mayar da hankali ga sana’ar dinki domin hutar da Inna irin dawainiyar da take sha a kan mu.
Ubangidana yana kyautata min kwarai albarkacin maraicina. Muna matukar girmama kwastomanmu Alhaji Nababa Jatau, saboda yana kawo mana aiki a kan kari.
Sannu a hankali na shaku da shi har na fahimci irin burinsa na tsayawa takarar shugabancin karamar hukumarmu, lokacin kuwa gangar siyasa ta fara kadawa.
Yayin da guguwar zabe ta murtuke, ’yan siyasa suka zama tamkar zakuna wajen neman tagomashin masu kada musu kuri’a.
Ni kuwa tuni na yi kane-kane a cikin lamuran yakin zaben Alhaji Nababa Jatau, ya zamana ni ne sahun gaba wajen yada manufa a kafafen watsa labarai na zamani da sauransu.
Irin himmar da nake yi wajen taya shi kamfen ya sa na ajiye sana’ar dinki duk da dimbin nasihohin da maigidana yake yi min.
Ba shi ba ma, hatta Innata tana yawan gargadina a kan biye wa ’yan siyasa. Ni kuwa gani nake yi ba su fahimci rayuwa ba ne.
Wani lokaci Inna tana nuna amincewa da ra’ayoyina kan siyasa da zaben Nababa Jatau, cewar shi ne mafi alheri gare mu da yankinmu.
Wani lokaci kuma takan yi kokwanto da irin romon da nake mata albishirin za mu kwasa idan ya haye zaben.
“Yanzu kana nufin idan ya ci zabe za ka dawo sana’ar dinkinka?” Wata rana ta tambaye ni bayan na gama yi mata albishirin da na saba.
Na juya hannu na watsar ina cewa, “Haba Inna, sabuwar duniya ta samu wa yake ta dinki kuma? Ai da zarar ya haye zaben nan to gida na musamman zan gina mana. Na yi aure, na aurar da Habiba, kuma na kai ki Makka.”
Irin wadannan buruka da wasunsu suke sake ingiza ni wajen ganin mun yi nasara. Sannu a hankali sunana ya rikide daga Rabi’u Dan Atine Gurguwa ya koma Rabi’u NJ.
Zabe ya tunkaro saura kwana kalilan, don haka muka sake zage dantse rai da buri bisa ganin mun samu nasara.
Ni ne kan gaba wajen kawo wa mutanen unguwa kayan masarufi domin jan hankalinsu.
Ina cikin masu bin malamai da ’yan tsibbu domin neman sa’a. Kuma ni ne ‘lambawan’ wajen jagorantar matasa wajen kaddamar wa ’yan adawar da suke hamayya da mu.
Don haka babu jimawa sunana ya tumbatsa, kowa ya san ni kuma ya san irin manufata. Takena shi ne, “A ba mu a huta, a bi mu a ji dadi.”
Ranar zabe ban zauna ba, ballantana na huta. Muka yi ta zirga-zirga tsakanin rumfa zuwa rumfa domin neman nasara.
Tsakar dare aka kammala tattara sakamakon zabe aka sanar da cewa gwaninmu Alhaji Nababa Jatau ya samu nasara.
Haba! Wannan rana ta zama ta musamman gare ni har nake ganin ko na gaban Ka’aba bai fi ni farin ciki ba. Ashe ban sani ba, wannan murna ce farkon matsalar rayuwata.
Gaskiyar masu azanci da suke cewa masoyi yakan rikida zuwa makiyi. ’Yan siyasar zamani ba su san martabar alkawari ba.
Sannu a hankali dangantakata da Alhaji Nababa ta rika tabarbarewa, tun ina iya samun ganin sa ya yi min dadin baki har ya zamana ba ni da ikon ganin sa.
Duk lokacin da na je ofis wajensa sai a ce min yana da uzuri. Gida kuma kullum na je sai a ce ba ya nan.
Wata ranar juma’a na yi dirshan har sai da na jira lokacin da ya fito daga ofis domin zuwa gida.
Yana gani na ya hade fuska kamar girar saniya. Na basar kamar ban gani ba. Na ce da shi, “Honorabul har yanzu fa ina tuni. Alkawurran nan dai har yanzu ba su tabbata ba.”
Ya bude baki da kyar ya ce, “Muna nan muna duba inda za mu saka ka ne. Saboda ba ka da takardu masu kyau. Kuma sakandare ne ba zai maka wani amfani ba.” Na hasala na ce, “Amma yaya ba ka taba gaya min haka a baya ba sai yanzu? A kan me…”
“Kai.” Ya katse min magana. “Ina sauri zan yi mitin da gwamna. Idan na samu dama zan kira ka.”
Kafin na ci gaba da magana tuni ya shige motar gwamnati. Jami’an tsaro sun yi mana banga-banga tsakani.
Cikin tsananin bacin rai da takaici na kudunduno wani wawan zagi da muke yi wa ’yan adawa na dirka masa. Na tabbata ya ji abin da na fada, amma ya yi biris bai ko kalle ni ba.
Haka na tafi gida cike da bakin ciki da bacin rai. Babban takaicina yadda abokan adawar da muka buga da su muka kayar da su yanzu su ne ’yan lele a wajensa.
Na tafi gida, na tarar Inna tana kwance ba lafiya. Cikin sauri na tafi nemo mata magani a kemis.
Daidai lokacin da na sawo maganin na juyo zuwa gida wata motar jami’an tsaro ta tsaya gabana.
Wasu zaratan jami’ai suka yo kaina cikin shirin yaki, suka kewaye ni. Na tsaya cik cikin tsoro da fargaba. Nan da nan suka damke ni suka cusa cikin motarsu.
Kwana uku ban san inda kaina yake ba, kuma ban san halin da Innata take ciki ba.
Babu wanda ya ce da ni kanzil in ban da wani busasshen biredi da ake ba ni a kullum, sau biyu.
Ranar Litinin aka gurfanar da ni gaban kuliya. A nan ne aka karanta min laifina, wai na ci mutuncin shugaba.
Nan take na musanta haka, na so a ba ni dama na fadi irin uzurina ban samu wannnan ikon ba.
Alkali ya yi umarnin a kai ni gidan horo zuwa wani lokaci na gaba da za a waiwaye ni.
Jin haka na barke da kuka ina rokon su bari na je na ga halin da Innata take ciki, amma ba wanda ya saurare ni.
Haka na shiga jarun cikin tsananin damuwa da takaicin yadda ruwa ya dafa kifi.
Shekara guda ina tsare, ana ta kaiwa da komowa sakamakon rashin gabatar da hujja daga masu tuhuma da kuma taurin kaina na kin amincewa da zargi.
Da taimakon kungiyoyin kare hakkin dan Adam aka kori karar saboda babu hujja.
Komawa ta gida ke da wuya na tarar da wani bakin lamarin da ya rusa min duk wani shiri da na yi na kalubalantar tsohon ubangidana Alhaji Nababa Jatau.
Na ga an fito da makara mutane sun yi sahu za a yi sallar gawa. Mutane suka rika yi min gaisuwar ta’aziyya cikin alhini.
Nan da nan na fahimci ashe Innata ce ajalinta ya sauka. Ban taba shiga duhun bakin ciki da tashin hankali kamar na wannan rana ba.
Na zauna makoki jama’a suka yi ta zuwa suna yi min gaisuwa tare da ba ni labarin abin da ya wakana yayin da nake tsare.
A nan na fahimci irin dawainiyar da makwabcinmu Alhaji Saleh ya yi da innata da kanwata lokacin da ba na nan.
Muna da sabanin fahimta kan siyasa, ban taba tsammanin wani abin alheri daga gare shi ba.
Wannan ya sa na kara fahimtar tsarin dimokuradiyyarmu cewar biyayya ga ’yan siyasa daban, cika alkawarin ’yan siyasa daban.
Ranar sadakar uku mutane suka taru aka yi addu’a. A ranar ne na samu ziyara daga manyan mutanen da muka yi mu’amala a baya.
Hatta ’yan adawa da yawa sun zo mini ta’aziyya da kuma jaje. Daya daga cikinsu ya ba ni makudan kudi da nufin jan hankalina na yi masa kamfen irin yadda na yi wa Alhaji Nababa a baya. Ni kuwa tuni na dawo daga rakiyar jiran kahon jaki.
Daga abin da na samu na shiga saye da sayarwa na kayan dinki. Sannan kuma na soma gyaran keken dinki.
Har ila yau na sayo kekunan yara na yin dinki, ana biyan su lada.
Shafukana na Fesbuk da Instagram, suka tashi daga na tattaunawar siyasa zuwa na kasuwanci.
Na gina rijiya matsayin sadaka ga iyayena. Na hado kan sauran kannena kowa na ba shi aikin yi kuma na saka su a makarantu.
Tuni na yi hankali, kuma na fahimci cewa akasarin ’yan siyasar kasar nan sun fi tinkaho da karya, kuma suna fakewa karkashin dimokuradiyya suna cin karensu babu babbaka.
Ba zan taba mantawa da innata ba, kuma ba zan taba mantawa da Nababa Jatau da irin sakamakon da ya yi min ba.
Yanzu kai kana ganin zan sake yarda na yi saki-reshe-na-kama-ganye ga dimokuradiyyar makaryata da ba su san darajar gaskiya da wulakancin karya ba?
Ni dai a ganina, sana’a ita ce kadai dimokuradiyyar talaka.