Shugaban Kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco, ya yi zargin cewa wasu masu safarar miyagun kwayoyi da aka taba yankewa hukunci ne suka kitsa yunkurin kifar da gwamnatinsa wanda bai yi nasara ba.
Shugaban dai ya zargi wani tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa na kasar da ake zargi da alaka da wasu ’yan kwayar da zama kanwa uwar gami a yunkurin juyin mulkin.
- Amurka ta bukaci ’yan kasarta su gaggauta ficewa daga Ukraine
- PDP ta jadadda dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo a Kano
A ranar daya ga watan Fabrairun 2022 ne dai wasu masu dauke da makamai suka yi yunkurin yin juyin mulki a daidai lokacin da Shugaban ke tsaka da jagorantar taron Majalisar Zartarwar kasar.
Daga bisani dai Shugaban ya shaida wa maneman labarai cewa ya tsallake rijiya da baya a harin wanda aka kwashe tsawon sa’o’i biyar ana musayar wuta sannan aka kashe mutum 11, yawancinsu jami’an gwamnatinsa.
Tuni dai aka kaddamar da bincike kan wadanda aka kama kuma ake zargi da hannu a yunkurin, cikinsu kuwa har da Admiral Jose Americo Bubo Na Tchuto, tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwan da hadimansa; Tchamy Yala da Papis Djeme.
Sai dai duka mutum ukun sun musanta hannu a zarge-zargen a gaban wata kotu da ke Amurka.
Kotun dai ta yanke wa Bubo hukuncin daurin shekara hudu, yayin da su kuma Tchamy da Papis aka yanke musu shekara biyar da shekara shida.
Duka su ukun dai daga bisani sun koma Guinea-Bissau bayan an sake su.
A cewar Shugaba Umaro dai, “Yayin juyin mulkin, na gansu da idanuna. Sun so ne su kashe ni sannan su kashe Fira-Minista da duk kusoshin gwamnatina.
“Lokacin da suka fara harbe-harbe a Fadar Shugaban Kasa, Bubo na hedkwatar sojojin ruwa, kuma na ji su suna cewa za su kira shi don ya turo musu karin dakaru,’ inji Shugaban.
Umaro Sissocohar ila yau ya yi zagin cewa mutanen sune kuma suka kashe tsohon Shugaban Kasar, João Bernardo Vieira, a shekara ta 2009.
Ya kuma ce akwai hannun wasu ’yan tawaye daga yankin Casamance na kasar Senegal.