✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dhaka ya ja kunnen Wenger

Sabon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila, Granit dhaka ya yi gargadi ga kocin kungiyar, Arsene Wenger cewa ba zai amince ya rika…

Sabon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila, Granit dhaka ya yi gargadi ga kocin kungiyar, Arsene Wenger cewa ba zai amince ya rika ajiye shi a benci ba, ba tare da wani dalili kwakkwara ba.
Shi dai dhaka wanda ya canza sheka daga kulob din Borussia Monchenglabach na kasar Jamus zuwa kulob din na Arsenal a kakar wasa ta bana ya nuna ya koma Arsenal ne don ya rika yin wasa a kan kari ba tare da an ajiye shi a benci ba.
dhaka dan asalin kasar Suwizilan ya koma kulob din Arsenal ne a kan Fam miliyan 30, kuma kawo yanzu ya buga wasanni da dama ga kulob din na Arsenal.