✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dembele na son komawa Arsenal

Rahoton da jaridar Don Balon da ake bugawa a Sifen ta fitar a ranar Talatar da ta wuce, ya ce dan kwallon gaba na kulob…

Rahoton da jaridar Don Balon da ake bugawa a Sifen ta fitar a ranar Talatar da ta wuce, ya ce dan kwallon gaba na kulob din FC Barcelona, Ousmane Dembele yana sha’awar canja sheka zuwa kulob din Arsenal da ke Ingila a karshen kakar wasa ta bana.

Dembele wanda ya canja sheka a bara daga kulob din Burossia Dortmund na Jamus zuwa na FC Barcelona da ke Sifen a kan Fam miliyan 100, ya kasa samun gindin zama a kulob din ne saboda yawan raunin da yake ji.

dan shekara 20, Dembele ya ji rauni a wasansa na farko da ya fara yi wa Barcelona a gasar La-Liga ta Sifen a bana.  A ranar da ya buga wasan da kulob din ya yi da na Getafe ya samu raunin da ya sa ya kwashe wata hudu yana jinya.

Rahoton ya nuna ganin yadda bai samu gindin zama a kulob din Barcelona ba ya sa yake yunkurin komawa Arsenal don ya hadu da takwaranrsa Pierre-Emeric Aubameyang da suka yi kwallo tare a Dortmund.

Tuni dan kwallon ya nemi mahukunta Arsenal da su yi duk mai yiwuwa don ya koma Ingila da buga kwallo.