Wani deliget din Jam’iyyar APC daga Jihar Jigawa, Isa Baba Buji, ya rasu yayin da yake shirin halartar filin zaben fid-da-gwanin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a Abuja.
Buji, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa ya rasu ne da yammacin ranar Talata a Abuja.
- Ina makomar Sha’aban Ibrahim Sharada a Siyasar Kano?
- EFCC ta girke jami’ai a wurin zaben dan takarar shugaban kasar APC
Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa, Bashir Kundu ya tabbatar da rasuwar deliget din inda ya ce “Ya rasuwa da safiyar Talatar nan.”
Rahotanni sun bayyana cewa daliget din ya yanke jiki ya fadi ne a Ofishin Hulda da Jama’a na APC da ke Abuja, lokacin da yake shirin zuwa wurin zaben fid-da-gwanin shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga ’yan uwan mamacin a shafinsa na Twitter.
Sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Laolu Akande, ya wallafa ta ce, “Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya bayyana damuwarsa da samun labarin rasuwar daya daga cikin deliget din APC daga Karamar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa, Isa Baba Buji mai shekara 61.
“Yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai, gwamnati da daukacin al’ummar Jihar Jihar.”
Kafin rasuwarsa Buji, ya kasance Mataimakin Shugaban yankin Kudu maso Yammacin Jihar Jigawa.