DCP Abba Kyari ya kasance shahararren hafsan dan sanda mai yaki da manyan laifuka inda yake jagorantar runduar ’yan sanda ta musamman a wannan aiki.
Ya kasance dan sandan da ake kallo a matsayin amintacce mai dabi’ar ‘ba sani ba sabo’ da jagorancinsa na Rundunar Tara Bayanai ta ’Yan Sanda (IRT), wajen bin maboyar masu aikata laifuka yana kama su.
- NAJERIYA A YAU: Abin da Abba Kyari Ya Fada Kafin A Kama Shi
- ’Yan sanda sun cafke Abba Kyari sa’o’i bayan NDLEA ta ba da shelarsa
Sabanin wasu jajirtattun ’yan sanda da ba a jin labarin ayyukansu, labarin Abba Kyari ya karade ko’ina, ga shi kuma yana rauywa ta kasaita, abin da wadansu ke ganin shi ne musabbabin farko na sanya alamar tambaya a kansa.
Abba Kyari ya fara tashe ne a 2011, bayan Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas ta nada shi ya jagoranci tsohuwar Rundunar ta Musamman Kan Yaki da Fashi (SARS).
Abin da ya jawo masa suna shi ne yadda ya rika bankadowa yana tarwatsa masu aikata manyan laifuka yana kama su, kama daga masu garkuwa da mutane zuwa ’yan fashi da masu damfara ta intanet da sauransu.
Tarihin DCP Abba Kyari
An haifi Abba Kyari ne a shekarar 1975 kuma dan asalin Karamar Hukumar Gujba ne a Jihar Yobe.
Amma ya taso ne a garin Maiduri, hedikwatar Jihar Borno, inda ya yi karatu har zuwa matakin jami’a, inda a 1997 ya samu digirinsa na farko a fannin Tarihin Kasa daga Jami’ar Maiduguri.
Ya yi aikinsa na yi wa kasa hidima a Jihar Akwa Ibom, wanda ya kammala a 1998.
Shigarsa aikin dan sanda
Ya fara aikin dan sada ne a 2000 a matsayin Mataimkain Sufurtandan Dan Sanda, bayan kammala Kwalejin Kananan Hafsoshin ’Yan Sanda.
Ya yi aiki a Kananan Hukumomin Song, Girei da Numan a Jihar Adamawa, inda a nan ya fara kafa tarihi.
Manyan nasarori
Ya fara yin tashe ne a yankunan bayan da ya kama wani hatsabibin dan fashi mai suna ‘Ndagi’ wanda aka fi sani da Spirit.
Spiriti yi shafe shekaru yana addabar Numan, gari na uku mafi girma a Jihar Adamawa, kafin daga bisani ya shiga hannun Abba Kyari.
Shi ne kuma ya kama jagoran masu garkuwa da mutane a Jihar Legas, wato ‘Evans’ da kuma Hami Wadume a Jihar Taraba.
Sannan shi ne ya jagoranci aikin kubutar da Magajin Garin Daura a Kano. Basaraken ya kasance suruki ga hadimin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
DCP Abba Kyari ya dade yana tashe, har a kafafen sada zumunta, a matsayin dan wani sanda daya tamkar da 10 kuma jarumi.
Ya samu wannan matsayi ne saboda yadda ake yayata nasarorinsa wajen bin diddigi da bankado masu aikata manyan laifi da kuma kama su cikin nasara.
Badakalar Hushpuppi
A watan Agustan 2021 guyawun masoyansa suka fara sanyi, bayan bayyanan alakarsa da fitaccen dan damfara ta intanet, Ramon Olorunwa Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka (FBI) ce ta fitar da rahoton a binciken da take yi kan zargin damfara ta Dala miliyan 1.1 da Hushpuppi ya yi, wanda ake zargin Abba Kyari na da hannu a ciki.
Zargin na FBI ba shi ne irinsa na farko da aka yi masa na bayar da kai bori ya hau ba. Bisa alamu kuma ba shi ne na karshe ba, ganin yadda wata sabuwar badakalar ta ta dabaibaye shi.
A baya, an sha zargin rundunar da yake jagoranta da tauye hakkin dan Adama, cin zalin mutanen da ake zargi, da kuma karkatar da kadarorin da suka kwato.
A lokacin da labarin alakarsa da Hushpuppi ya fara fitowa, Abba Kyari ya musanta, amma daga baya ya rika sauya maganarsa a kan batun.
Aminiya ta gano akalla sau 12 da ya yi kwaskwarima ga nasa bangaren labarin da wallafa a shafinsa na Facebook.
Badakalar ta Hushpuppi ta sa Hukumar ’Yan Sandan Najriya ta dakatar da shi daga aiki, ta kafa kwamitin bincike kan zargin.
Sai dai wata shida bayan nan, hukumomin ba su kai ga cim-ma matsaya a game da makomarsa ba, wanda ya sa masu sharhi suke zargin akwai lauej cikin nadi.
A yayin da yake jira ya san makomarsa kan zargin Badakalar Hushpuppi, sai ga wani babban zargi daga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da ke alakanta shi da masu fasakwaurin miyagun kwayoyi.
Duk da cewa ya musanta zargin, NDLEA ta fitar da wani bidiyo da ta kafa hujja da shi na hannunsa, kuma tuni har hukumar ta yi awon gaba a shi domin bincikar sa.
Wannan zargi na karshe dai ya riga tambara shi yana kuma neman kara ruguza kimarsa a idon duniya, sabanin yadda a baya ake ganin shi a matsayin kwararren dan sanda abin buga misali.