✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daya cikin fursunonin da suka tsere daga kurkukun Katsina ya shiga hannu

A kwanakin baya ne suka tsere daga gidan

An sake kama Abba Kala, daya daga cikin fursunonin nan da ke zaman jiran hukunci kuma ya tsere daga gidan gyaran hali na Katsina da ke Jihar Katsina.

Abba dai shi ne babban wanda ake zargi da kitsa tserewa daga gidan gyaran halin a ranar 17 ga watan Oktoban da ta wuce.

Samun nasarar kamun ta biyo bayan wani bincike da aka gudanar tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro a jihar ta Katsina.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) da ke Jihar Katsina, ASC Najibullah Idris, ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

Ya kuma ce an kama sauran fursunonin da suka gudu ta hanyar amfani da tsarin sa ido na kwakwaf da kuma hadin gwiwa da wasu jami’an tsaro wanda hukumar kula da gidajen ta ce za a sake tsare shi bisa wata kulawa ta musamman.

A cewar Kakakin, “Babban Kwamandan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, Haliru Nababa, ya yaba wa sauran jami’an tsaron bisa hadin kan da ya kai ga sake kama shi, kuma ya tabbatar wa jama’a cewa babu wani abin fargaba saboda halin da ake ciki.

Najibullah ya kuma ce yanzu haka sun baza komarsu suna neman wani wanda suka tsere tare da Abba Kalan.

Idan za a iya tunawa, an kama Abba Kala ne bisa zargin aikata fashi, boye makamai da kuma sayar da motocin sata gami da hada baki da sauran barayin da suka addabi al’ummar Jiahar wajen yi masu fashi da makami.

Wannan kamu ba shi ne na farko da rundunar ’yan sanda ta yi mashi ba, sai dai wannan karon ta kai ga ajiye shi a gidan gyaran halin da kotu ta yi kafin yanke mashi hukunci.