✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daurawa: Matsayin malamai kan dokar tantance masu wa’azi

A kwanan nan ne sanannen malamin Musulunci a jihar Kano, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bukaci gwamnoni musamman na arewacin Najeriya su yi dokar tantance…

A kwanan nan ne sanannen malamin Musulunci a jihar Kano, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bukaci gwamnoni musamman na arewacin Najeriya su yi dokar tantance yadda malamai ke gudanar da wa’azi.

Dokar, a cewarsa za ta shafi masu wa’azi na Musulmai da Kirista, domin ware wadanda suka cancanta da kuma ba su izini, yana mai alakanta yawan rikice-rikicen addini a yankin da ayyukan masu wa’azin da ba su cancanta ba.

Wasu malaman na da sabanin fahimtar Malam Daurawa wanda ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su rika tace irin malaman da suke ba wa damar yin wa’azi ta kafafen na su.

Aminiya ta ji ra’ayin wasu malaman Musulunci a kan matakin da malamin ke kira a dauka.

Bai dace a bar harkar addini kara zube ba —Arzai

Wani babban malami a Kano, kuma tsohon Mataimakin Kwamandan Hisba Bangaren Ayyuka na Musamman, Shaikh Muhammad Nura Muhammad Arzai ya ce dama su tun da farko sun dade suna goyon bayan a yi dokar.

“Ko a lokacin ina Hukumar Hisba, na nemi a kafa irin wannan dokar, saboda munanan abubuwan da ake yadawa musamman a kafafen yada labarai suna taimakawa wajen yaduwar barna”, a cewar Shaikh Arzai.

Ya kara da cewa, “A fahimtarmu da addini, bai kamata a bar mutane a sake, da wanda yake da ilimi da wanda ba shi da shi a ce a saki kowa ya yi magana a harkar addini ba.

“Yanzu likitoci alal misali, ‘yan jarida da injiniyoyi ai ba su bar harkarsu sasakai, kara-zube kowa ya sa baki ba. To don me za a ce sai harkar addini ce za a bari babu tsari?

Ina goyon bayan tantance masu wa’azi

“Saboda haka ina goyon bayan ya kamata a tantance wadanda za su rika wa’azi da kuma abin da za su rika wa’azin a kai.

“Allah Madaukakin Sarki da kanSa a Alkur’ani Ya fada cewa babu abin da mutum zai fada sai masu rubutu (Rakib da Atid) sun rubuta, Ya kuma gargade mu kan fadin abin da ba mu da ilimi a kai cewar hakika jinka da ganinka da kuma zuciya da gabobi gaba daya dukkansu ababen tambaya ne.

“Kazalika Annabi (SAW) ya ce da wani sahabi ka kare wannan (ya yi nuni da harshensa) saboda ya nuna mana illar harshe”, inji Shaikh Arzai.

Malamin, wanda jigo ne a Darikar Tijjaniyya kuma Sakataren Majalisar Limamai ta Jihar Kano, ya ce ba harkar wa’azi kadai ya kamata a yi wa doka ba, hatta sojojin baka da suke shiga kafafen yada labarai suna magana a shirye-shiryen siyasa da masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani su ma suna bukatar makamanciyar wannan dokar don a tsaftace abin da mutane su ke sauraro.

Kirkiro da wasu sharudda bai dace ba

Sai dai a nasa bangaren, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triumph da ke Kano, Shaikh Lawal Abubakar ya ce addinin Musulunci yana da tsari matuka.

“Musulunci addini ne da da’awa, shi ya sa ma Manzo (SAW) ya ce ‘ku isar min (da sako na) ko da da aya daya ce’, to sai dai Allah Ya ce ku yi da’awar da hikima da kuma wa’azi kyakkyawa; Idan wannan Shaikh Daurawa yake nufi, to hakan addini ma ya yi na’am da shi.

“Dama akwai shi a addini, sai dai wanda ka ga ba ya amfani da shi ko dai kan rashin sani ko kuma son zuciya.

“Amma idan yana nufin doka ko wasu sharudda da gwamnati ce za ta kirkiro, to hakan ba zai dace da Musulunci ba.

“Dalili kuwa shi ne saboda ‘yan siyasa suna da ra’ayoyinsu kuma za su iya kunso wasu abubuwan da za su taimaka wa wadannan manufofin [wanda] hakan kuma zai iya sa a dakile duk wanda aka san ba ya ra’ayin wannan dan siyasar.

‘Za ta dakile hanyoyin alheri’

“Amma ina da ra’ayin cewa idan wani ya yi amfani da mumbarinsa na wa’azi ya ci mutuncin wani, to babu laifi wanda aki ci mutuncin nasa ya kai kotu ya bi hakkinsa, amma ba na goyon bayan wai a ce gwamnati ce za ta kawo wasu sharudda da dokoki da sunan dokar addini.

“Wannan ba zai yiwu ba a Najeriya saboda zai kawo barna, zai dakile hanyoyin yada alheri a madadin a ce mutane suna wa’azi suna isar da sakon Allah a duk inda suka sami dama”, inji Shaikh Lawal Abubakar.

Wasu masana da malamai dai sun dade suna alakanta wasu rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci a Najeriya da yadda kowa yake da damar yin wa’azi ba tare da tantance ingancin abin da zai fada wa mabiyansa ba.

Ko a shekarun baya sai da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi makamanciyar wannan dokar a jiharsa da nufin yi wa tufkar hanci, duk da dai dokar ta fuskanci tirjiya da suka daga jama’a da malaman addinai daban-daban.

Yawancin masu tir da dokar dai na ganinta a matsayin wani tarnaki ga ‘yancinsu na addini da kuma fadin albarkacin baki, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar musu.