✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daukar hoto tsirara a gaban ‘bishiya mai tsarki’ ya jawo wa ’yan Rasha kora daga Indonesia

Indonesia dai ta ce za ta mayar da mutanen kasarsu

Kasar Indonesia za ta fatattaki wasu ma’aurata ’yan kasar Rasha daga cikinta saboda daukar hoto tsirara a jikin wata bishiya mai tsarki da ke Birnin Bali na kasar.

Ofishin shige da fice na kasar a ranar Juma’a ya ce zai mai da ’yan kasar mata da miji ne zuwa gida, bisa laifin daukar hoto tsirara a jikin wata tsohuwar bishiyar mai tsarki a yankin Tabana na kasar.

Matar mai suna Fazleeva wacce fitacciya ce a duniyar sada zumunta tare da mijinta, Andrey dai sun sanya hoton a shafinsu na Instagram, kuma hakan ya bata ran masu ruwa da tsaki na kasar.

Shugaban hukumar Shige na kasar Jamaruli Manihuruk ya fitar da wata sanrwa kan hakan inda ya ce bayan maida su kasarsu, an hana su shigowa Indonesia tsawon wata shida.

Ma’auratan dai sun amsa laifinsu tare da neman afuwa, musamman a shafukansu na sada zumunta, inda suke da dimbin magoya baya.

Yankin na Bali dai ba wannan ne karon farko da ya fara korar wadanda suka sabawa al’adarsa ba.

Ko a watan Afrilun da ya gabata dai an yi hakan ga wani dan kasar Kanada da ya yi rawa tsirara a dutsen Batur.