Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) za ta fitar da jerin sunayen mutum 5,000 da suka ci jarabawar daukar aikin da ta gudanar.
Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Abubakar Audi, ya ce za ta fitar da sunayensu daga ranar Litinin 17 ga watan Janairun da muke ciki.
- ‘Na dauki ci da sayar da sassan jikin mutane a matsayin al’ada’
- Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba
Ya bayyana cewa daga ranar Litinin din mutanen da suka zana jarabwar za su iya duba sunayensu ta shafin hukumar, sannan za a fara tantance dakardun wadanda suka yi nasara a ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki, gabanin fara ba su horo.
Da take bayani, Sakatariyar Majalisar Daraktocin Hukumomin Sibil Difens, Kashe Gobara, Shige da Fice da Gidajen Yari, Aisha Rufai, ta ce, “Mutum 5,000 ne suka yi nasara. Yanzu matakin da muke ke nan. Kuma daga yau za mu fara aikin tantance su.”
Ta kuma kore fargabar da ake yi na cewa za a soke batun daukar aikin da aka faro shi tun daga shekarar 2019.
A cewarsa, ’yan Najeriya miliyan 1.5 suka nemi aikin da hukumar take da gurabun aiki 5,000.
“Zuwa watan Disamban 2020 kuma mutum 53,116 daga cikinsu masu neman aikin suka sabunta takardunsu.