✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattijuwar da ta fi kowa tsufa a duniya ta rasu tana da shekara 118

An haife ta ne ranar 11 ga Fabrairu, 1904 a garin Ales da ke kudancin Faransa

Bafaranshiyar dattijuwar da kungiyar bincike kan shekaru ta ce ta fi kowa tsufa a duniya Sister André ta rasu tana da shekaru 118 a duniya. 

Magajin garin Toulon Hubert Falco ne ya bayyana hakan ranar Laraba, inda ya ce ta samu kambun ne a watan Afrilun shekarar 2022.

An haifi marigayiyar ne a ranar 11 ga Fabrairu, 1904 a garin Ales da ke kudancin Faransa.

Margayiyar mazauniyar Kudancin birnin Toulon ce, kuma ta yi aiki a matsayin malama mai koyarwa a gida, kuma sai da ta shekara 40 ta karbi addinin Kiristanci.

Kafin rasuwarta sai da Sister Andre ta koma amfani da kujerar guragu kuma ba ta gani sosai.

Kundin adana tarihi na Guinness dai ya bayyana Lucile a matsayin ta biyu a jerin Faransawan da suka yi tsawon rai a duniya.