✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattijo mai shekaru 60 ya yi wa ‘yar shekara 5 fyade a Bauchi

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, ta cafke wani dattijo mai shekaru 60, Muhammad Dahiru da ya yi wa ‘yar shekara 5 fyade a…

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, ta cafke wani dattijo mai shekaru 60, Muhammad Dahiru da ya yi wa ‘yar shekara 5 fyade a kauyen Nahuta na karamar hukumar Toro ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmed Muhammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata.

DSP Wakil ya ce dattijon ya yaudari karamar yarinyar zuwa wani kango inda ya keta mata haddii tare da yi mata barazanar kashe ta muddin ta labarta wa wani abin da ya aikata.

“Iyayen yarinyar sun gano rauni da jini da ke fita daga gaban yarinyar kuma aka tabbatar da abin da ake zargi a babban Asibitin Toro”.

“Mun kama dattijon da ake zargi kuma za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike,” inji DSP Wakil.