✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattawan Kirista sun gargadi Tinubu kan raba kawunan mabiyansu a Arewa

Muna gargadin APC kan ta daina amfani da kudi tana haifar da rabuwar kawuna a tsakanin Kiristoci.

An gargadi Jam’iyyar APC da dan takararta na Shugaban Kasa, Bola Tinubu, kan su daina amfani da kudi suna raba kawunan mabiya addinin Kirista don biyan bukatunsu.

Wannan gargadi na kunshe ne cikin sanarwar da Kungiyar Dattawan Kirista ta Arewa ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun shugabanta, Oyinehi Inalegwu.

Kungiyar ta ce, “Muna gargadin APC kan ta daina amfani da kudi tana haifar da rabuwar kawuna a tsakanin Kiristoci, musamman ma a Arewa.”

Kazalika, ta yi zargin cewa baya ga batun tsayar da ’yan takara mabiya addini daya, APC da dan takararta Tinubu na kokarin yin amfani da wasu hanyoyi wajen raba kan al’ummar Kirista domin cim ma bukatarsu a Zaben 2023.

Kungiyar ta ba da misalin yadda a watan Disamba na 2021,  Tinubu ya gana da wata kungiyar Kirista tare da tallata mata batun takarar Musulmi da Musulmi.

“Don haka muna gargadin kowane dan takarar Shugaban Kasa ya guji takarar mabiya addini daya don kauce wa addinatar da lamarin tafiyar da kasa,” inji kungiyar.