✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan rayuwa goma daga bakin Ibni kayyim Al-Jawziyyah

Ya ku ma’abuta filin Sinadarin Rayuwa, gaisuwa gare ku, wacce ta kamace ku, Assalamu alaikum.Bayan haka, da ikon Allah, wannan makon ma za mu duba…

Ya ku ma’abuta filin Sinadarin Rayuwa, gaisuwa gare ku, wacce ta kamace ku, Assalamu alaikum.
Bayan haka, da ikon Allah, wannan makon ma za mu duba wani maudu’in mai take na sama. A wannan karon, za mu duba wani darasi ne, wanda muka kalato daga bakin mashahurin malamin malamai, Ibni kayyim Al-Jawziyya. Wannan bawan Allah, wanda ya dade yana amfanar da al’umma daga kogin iliminsa, ya kasance jigo wajen zizara wa duniya sinadaran ci gaba, sinadaran wayar da kai da saukaka jin dadin ruhi.
A wannan darasin, fitaccen malamin, ya zayyano wadansu jiga-jigan al’amura ne har guda goma, ya bayyana mana cewa kada mu yi sake mu yi watsi da su, kada mu banzatar da ganimar da ke tattare da su. Ya tsaya kai da fata, ya sanar da mu fa’idojinsu, kamar kuma yadda ya sanar da mu illar da ke tare da banzatar da su. Kamar yadda ya lissafa su, wadannan abubuwa kuwa su ne: Ilimi, ayyukan da muke aikatawa a kullum, dukiyar da muka mallaka kuma muke sarrafa ta, zuciyar da ke cikin jikinmu da kuma shi kansa gangar jikinmu. Sauran sun hada da, kauna da lokaci da basirar da Allah Ya ba mu da bautar da muke gabatarwa da kuma zikirin da muke gudanarwa yau da kullum.
Bari mu dauki wadannan jiga-jigan al’amura guda goma, daya bayan daya, mu bi kadinsu, sannan mu ga yadda za su kasance masu amfani gare mu, sannan kuma mu sake duba sakamakon da za su haifar mana ga rayuwa, idan muka banzatar da su, ko kuma muka gudanar da su ba yadda ya kamata ba.
Ilimi: Kamar yadda mashahurin malamin ya fada mana, ya nuna cewa ilimi wani babban al’amari ne, wata babbar baiwa ce da Allah Ya albarkaci mutum da ita. Ilimi yana taimaka wa dan Adam ne wajen gudanar da rayuwarsa cikin fa’ida. Tare da ilimi ne mutum zai kasance mutum na kwarai, wanda zai bambanta da dabba. Don haka ne ma yake da tsananin muhimmanci ga mutum ya mike tsaye, ya yi duk abin da zai yi domin ganin cewa ya mallaki ilimi. Idan kuwa ya kasance bai yi haka ba, to kuwa babu raba daya biyu, zai kasance kuntukurmin jahili, zai kasance koma baya ga dangi, zai kasance shashasha, marar amfani ga kansa, kuma marar amfani ga sauran al’umma. Ke nan dai babu wani abu ma da mutum zain mallaka, wanda ya kai kima da darajar ilimi.
Mashahurin malamin ya ce, sai dai ba nan gizo ke sakar ba, domin kuwa mallakar ilimi kuma wani abu ne daban, sannan kuma yadda mutum ya gudanar da shi, shi ma wani abu ne da ban. Kamar yadda ya kamata, duk wanda ya samu ilimi, to ya tabbatar da yin amfani da shi wajen tafiyar da al’amuransa na yau da kullum yadda ya dace. Komai yawan ilimin da mutum ya samu, madamar bai yi aiki da shi yadda ya dace ba, to kuwa lallai bai tsinana masa komai ba. Ilimin da ba a yin aiki da shi, ya zama asara goma da goma. Don haka, mu jajirce, mu tsaya kai da fata, tare da hikima da basira, mu tabbatar da cewa duk abin da muka sani na ilimi, to mu aiwatar da shi a aikace, yadda za mu amfani rayuwarmu da ta al’ummarmu gaba daya. Domin kuwa mai ilimin da ba ya aiki da shi, kamar jaki ne da aka loda wa kayan littattafai. Ga shi dai da kayan ilimi niki-niki, amma ba zai amfanar da shi da komai ba. Abin koyo daga wannan bayani shi ne, mu bambanta kanmu daga jakin da ke dauke da littattafai, mu zamanto masu aiki da ilimin da Allah Ya ba mu.
Ayyukanmu: Aiki mai dadin fada, amma da wahalar aiwatarwa. A kullum dan Adam yana cikin aiki da hidima, domin kuwa jiki da jini, dole yake motsawa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, aiki ya bambanta zuwa kala biyu. Akwai aikin kirki, akwai kuma aikin baban giwa. Duk aikin da za mu gudanar, mu tabbatar da cewa aiki ne da zai amfane mu, ba wanda zai cutar da rayuwarmu ba. Duk aikin da za mu aiwatar, mu tsaya mu yi tunani a kansa, mu tabbatar da cewa mun aiwatar da shi da kyakkyawar niyya da manufa ta kirki. Ita kuwa rayuwa, madamar ba a gudanar da ita cikin fa’ida ba, to kuwa lallai an yi abin da ake kira da shukar dusa, ko kuma kamar abin da Hausawa suka kira da zuwan kare a karofi, babu rini balle matsa. Fa’idar wannan bayani shi ne, malam yana nufin cewa, mu tabbata mun gudanar da aikin kirki mai fa’ida ga rayuwarmu, mu guji yin aikin baban giwa.
Za mu ci gaba