✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan rayuwa daga labarin mai mata hudu

A wannan karon ma, mun samu gudunmuwar wannan labari ne daga fasihin marubuci, Malam Nasir G. Ahmad, Kano (08065496902). Ga labarin:An yi wani babban sarki…

A wannan karon ma, mun samu gudunmuwar wannan labari ne daga fasihin marubuci, Malam Nasir G. Ahmad, Kano (08065496902). Ga labarin:
An yi wani babban sarki da ke da mata hudu. Matarsa ta hudu, ita ce wadda ya fi matukar so da kauna, yake yin duk abin da zai faranta mata rai.
Ta ukunsu ita ma yana son ta sosai, sai dai kullum cikin fargabar za ta bar shi ta je ta auri wani yake.
Ta biyunsu kuwa, ita ce wadda yakan koma gare ta yayin tsanani don neman mafita, ta ba shi shawarwari tare da kwantar masa da hankali.
Ita kuwa matarsa ta farko, ya jingine ta ne gefe guda, ba ya ba ta kowace irin kulawa, yana hana ta hakkokinta, alhali tana matukar son sa, tana kuma taka rawar gani sosai wajen tabbatar mulkinsa.  
Ana nan kan haka sai wannan sarki ya kwanta cutar ajali. Ya tabbatar ba zai tashi ba, ga shi kuma ba ya son tafiya kabari shi kadai. Sai ya kira mowarsa (matarsa ta hudu) ya ce da ita:
“Ya ke sarauniyata, macen da na fi kauna, ke ce mafificiya cikin dukkan matana; ke nake ba wa kulawar da ta zarce ta kowacce. Kin ga dai halin da nake ciki yanzu. Ina so ki bi ni cikin kabarina don mu ci gaba da zama tare.”
Ita kuwa ta duba yanayin mijinta, ta ga irin tagayyarar da ya yi saboda ciwo. Ita kuwa ta duba yadda take cikin koshin lafiya, ga dukiya; sai ta ji a ranta cewa ai a lokacin ne ma take bukatar sabuwar rayuwa. Don haka sai ta yi tsalle wuri guda ta ce:
“Sam! Wannan abin da ba zai taba yiwuwa ba ne, iyakar rayuwarka daban, ni ma tawa daban. Kwanuka da shekarun da ka debo daban, haka ni ma nawa daban, saboda me zan bi ka kabari?” Ta juya ta yi tafiyarta ta bar shi nan cikin tsananin ciwo.
Sai ya kira matarsa ta uku, ya nemi ta amince ta bi shi su zauna a kabari tare. “Ina son ki amince da mu tafi tare, saboda irin zaman dadin da muka yi da ke a nan duniya.” Inji shi.
Ita kuwa sai ta ce: “A’a, ba da ni ba! In ka mutu waninka zai aure ni mu ci gaba da rayuwa.”
Sai ya kira matarsa ta biyu, wadda gare ta yakan koma yayin tsanani, ya fada mata wannan bukata tasa. Amma sai ta ce:
“Ka yi min afuwa. Ba zan iya amsa wannan bukata taka ba. Zan dai raka ka ka shiga kabarinka, ni na dawo.”
Sarkin nan ya cika da bakin cikin wannan butulci da matansa da yake kauna suka yi masa. Ga shi ba zai iya tunkarar matarsa ta farko da wannan bukata ba, musamman saboda ya san yadda yake musguna mata a yayin zamansu na aure kuma ba ma ya kula ta.
Can sai ya ji wata murya daga nesa tana cewa: “Ni zan bi ka na zauna tare da kai a duk inda za ka.”
Yana waigawa sai ya ga ashe matarsa ta farko ce. Amma ya ga yadda duk ta kanjame, ta kode, ta jeme, jikinta duk ya yi rauni saboda rashin kulawarsa gare ta. Ta samu wannan yanayi ne saboda rashin sukuni da rashin kwanciyar hankali da take raye a cikinsu a kullum.
Sarkin nan ya yi nadamar munanawarsa ga wannan baiwar Allah mai halacci, ya ce: “Abin da na yi miki ban kyauta ba. Da rayuwa za ta dawo min sabuwa, lallai da ba wadda zan kula da ita kamarki.”
’Yan uwa, ku sake natsuwa domin daukar darussan da ke labarin nan, domin kuwa ba sarkin nan kadai da ke bakin gargara yake da mata hudu ba! Kowannenmu yana da mata hudu kamar wannan sarki, ga karin bayani:
Mata ta hudu, ita ce jikinmu. Duk irin kulawar da za mu ba shi ta wankewa da shafe-shafe da kayan ado masu tsada da abinci mai kyau, rabon tsutsotsi ne in mun mutu. Iyakar amfanin jikinmu a nan duniya ne kadai, ba zai amfana mana komai ba a rayuwarmu ta kabari.
Mata ta uku, ita ce dukiyarmu da sauran kadarorinmu. Iyakar amfaninta a nan duniya ne, muna mutuwa za ta koma mallakar wasunmu. Da zarar mun mutu, magada za su shiga wawaso da rabo, wasu ma ba za a kare lafiya ba, sai an dangana ga alkali, domin rabawa.
Mata ta biyu, ita ce danginmu da abokananmu. Duk irin sadaukarwar da za su yi gare mu, abin da kadai za su iya yi gare mu bayan mun mutu, shi ne su kai mu kabari su dawo. Iyakarsu ke nan, amma babu wanda zai ce ya amince ya kwanta tare mu a kabari.
Mata ta farko, ita ce kyakkyawan aikinmu. Mukan shagaltu da yin sa, mu biye wa sha’awoyinnmu da dukiyarmu da abokanenmu, alhali kyakkyawan aikinmu ne kadai zai bi mu, ya zauna da mu a cikin kabarinmu.
To ya kamata mu rika kwatanta aikinmu yayin da ya zama mutum da za mu yi zaman kabari tare da shi, shin da wace irin siffa muke son ganin sa? Idan muka kula da kyakkyawan aiki, muka kyautata shi, zai yi kiba mulmul, ya zama abin sha’awa ga kowa, ya zama abokin zama a kabari. Amma idan muka munana shi, zai kasance kanjamamme, marar kyau, marar karfi; wanda ba zai iya tsinana maka komai ba a ko’ina, balle ma a kabari.
Ruwa a cokali, ya ishi mai hankali wanka. Allah Ya sa mu dace da rayuwa mai amfani, amin.