✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan da ke jibge a cikin Dare Dubu Da daya (2)

Ya ci gaba da cewa, ya kai wannan mutum da ka tsinci kanka a cikin wannan fada, ga gargadi zuwa gare ka, kada ka shagala…

Ya ci gaba da cewa, ya kai wannan mutum da ka tsinci kanka a cikin wannan fada, ga gargadi zuwa gare ka, kada ka shagala da al’amurran duniya, kada ka bari dadin cikinta ya rude ka, kada kuma ka bari wahalarta ta zautar da kai.

Ka sani dadin duniya ba mai dorewa ba ne, haka ma wahalar ta ba ta dorewa har abada. Duk abin da ka samu a cikinta tamkar bashi ne ka karbo, a kowane lokaci mai bashin nan zai iya karbe abinsa. Abin da duk ka gani cikin duniya tamkar mafarkin mai mafarki ne, kai, tamkar gulbin hamada ne ga mai jin kishirwa. Shaidan ke kawata maka duniya, kana ganin ta tamkar wata Aljanna, ba tare da ka farga ba har mutuwa ta riske ka.
Kada ka yarda da duniya, domin ita budurwar wawa ce, takan daga mutum sama daga karshe idan ya sakankance da ita sai ta sako shi kasa. Kada ka yarda da rudinta, kada ka yarda da zugar shaidani.
Misali na rayuwata kadai ya ishe ka gargadi; ni din nan in ji Basaraken, na mallaki garke dubu bisa dubu na dawaki. Na mallaki babbar fada. Ina da mata da sa-daka guda dubu, kyawawan gaske kamar watanni a daren sha biyu, dukkaninsu kuma ’ya’yan sarakuna ne. Ina da ’ya’ya dubu, dukkaninsu zakokin yaki ne. Na shekara dubu ina mulki kamar ba zan mutu ba. Na mallaki dukiya wadda ba ta da adadi kamar kasa, babu wani Sarki da ya tara irin dukiyar da na tara a lokacina.
Na shagala da rayuwa har ina ganin kamar ba zan mutu ba. Kwatsam, babu zato babu tsammani sai mai katse jin dadi ta auka mini. Mai raba da da mahaifi. Mai raba mata da miji. Mai raba tajiri da dukiya. Mai rushe gidaje da birane. Mai dauke babba da yaro. Mai raba uwa da jariri, wadda ba tausayin talaka don talaucinsa, mara tsoron Sarki da tajiri don karfinsu.
Bayan ya zo nan, sai ya ci gaba da jawabinsa, kamar yadda ake karantawa a jikin wannan allo, ya ce ka sani ya kai wannan mutum, mun rayu cikin wannan fada cikin tsauraran matakan tsaro da jin dadin rayuwa, ba mu ankara ba har Ubangijin sammai da kassai Ya turo mana jakadiyarsa, ita ce mutuwa. Ta shigo ta same mu a cikin wannan fada, ta rika daukar mu da biyu-biyu kowace rana. Askarawa ba su tsare ta daga gare mu ba. Dukiyoyinmu ba su fanshe mu daga wurinta ba. Mutane da yawa daga cikin mu suka mutu, muka zama tamkar muna cikin tekun mutuwa ne. Yayin da na ga haka sai na kira mai rubutu na umurce shi da rubuta baitoci dauke da gargadi a jikin dukkan allunan da ka gani cikin wannan fada, domin na baya su karanta, masu hankali daga cikinsu su hankalta, kafin lokaci ya kure musu.
Daga nan sai ya kara da cewa, ka sani ya kai wannan mutum, na mallaki rundunoni ta sadaukai masu karfi har runduna dubu bisa dubu. Kowace runduna akwai sadaukai dubu, mahaya dawaki. Kowane sadauki ya shiga sulke da buke da kwalkwali bisa kansa, a hannunsa na dama yana rike da takobi, yana walkiya. A hannunsa na hagu yana rike da mashi da garkuwa. A gindinsa ya soke wukake da kibau. Yayin da na ga mutuwa ta far mana, tana daukarmu da biyu-biyu kowace rana, sai na yi tsawa ga askarawa, na ce, “Me ya sa ba za ku yake ta ba, kuna gani tana kashe mu daya bayan daya?” Sai suka amsa mini, “Ta yaya za mu yi yaki da hukuncin Ubangiji, wannan da Yake da fada wadda ba mai gadinta, Sarkin da ke mulki ba tare da fadawa ba.”
Da na ji haka sai na ce, a kawo mini dukkan dukiyata. Aka kawo mini manya-manyan sundukai dubu bisa dubu na zinariya. Da wasu dubu bisa dubu na azurfa. Da wasu dubu bisa dubu na lu’u-lu’u. Da wasu dubu bisa dubu na sauran jauhari iri-iri. Aka tattaro garke-garke na dabbobi iri daban-daban. Ganin an kammala sai na ce wa askarawa, “Ku bayar da wannan dukiya dukkanta a matsayin fansar rayuwata ga mutuwar nan da ke son daukar mu.” Suka amsa mini, “Ba mu da wannan iko kan haka.” Na kara cewa, “Ku bayar da ita ku ce ta kara mini kwana daya a duniya.” Suka ce da ni, “Ba mu da wannan iko, wa ke da ikon karkatar da hukuncin Ubangiji?”
Daga sai na saduda, na tabbatar da ranar mutuwa askarawa ba su da ikon hanawa. Dukiya ba ta da amfani.’Ya’ya ba su kare ta. Abokai ba su tare ta. Daga nan ne sai mutuwa ta zo a sukwane, ta dauke ni, na zama kaskantacce bayan a da na kasance madaukaki a cikin jama’ata. Aka sanya ni a rami, aka mayar da kasa bisa kaina, bayan da na kasance ni ke yawo bisa kanta.
Daga nan sai ya sake dawowa zuwa ga mai karatu ya ce, ya kai mai karatu, ko ka san mai yi maka wannan gargadi da ke jikin wannan allo? Ba kowa ba ne face ni da ke cikin wannan kabari da kake kallo a cikin wannan shimfidaddiyar fada da ba irinta a doron kasa. Sunana Sarki Kush dan Sahaddadu dan Adi Babba.” Tamat!
Allah Ya sa mun amfana da wannan tsakure daga cikin littafin nan na tarihi, Dare Dubu Da daya. Darussan da ke jibge a ciki ba na jiya ba ne, ba kuma na yau ba ne kurum, darussa ne da ke tare da mu har zuwa gobe da za a nade shimfidar kasa, lokacin da za mu koma ga Maiduka, mu amsa tambayoyi kan abin da muka tara da yadda muka yi amfani da su. Allah Ya kara nuna mana gaskiya, a matsayin gaskiya domin mu ci gaba da bin ta, ita kuma karya ya fayyace mana ita, domin mu ci gaba da guje mata! Amin!