✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussan da ke jibge a cikin Dare Dubu Da daya (1)

Tun muna yara ba abin da ake horonmu da shi irin kada mu matsi littattafan da za su iya bata mana tarbiyya, musamman irin na…

Tun muna yara ba abin da ake horonmu da shi irin kada mu matsi littattafan da za su iya bata mana tarbiyya, musamman irin na Dare Dubu Da daya, wadanda a lokacin nan ba su wuce littafi na 1 zuwa na 5 ba. An ce ba komai cikinsa sai batsa da ashararanci. Kila shi ya sa ma ba a ci gaba da aikin fassara shi zuwa Hausa ba, kusan shekara 100 da soma aikin.
To amma da Allah Ya kai hannuna kan cikakken labarin Dare Dubu Da daya cikin Hausa, na shiga karatu tun daga dare na 1 zuwa yau da nake a dare na 570, sai na fahimci an yi wa wannan aikin littafin sanin damisar Bunu. Lallai akwai alamun batsa da sakin hannu wajen bayyana rayuwar mata da maza ko samari da ’yan mata, amma sai na kula cewa kashi 10 cikin 100 ne wadannan alamu suke ciki, kusan kashi 90, ilimi ne da fadakarwa da nusarwa. Karanta su kuwa zai kara wa yara sanin duniya da guje mata da ilimin yadda za su tunkari matsalolin rayuwa.
Littafin Dare Dubu Da daya cike yake da wakokin wa’azi da fadakarwa. Cike yake da jawabai masu ilimantarwa da suka shafi kimiyya da ilimin taurari da sanin labarin kasa da siyasa da addinin Musulunci da babbar lamari na rayuwa da mutuwa.
Abin da yau za mu yi shi ne, mu leka cikin wannan gagarumin littafi mu ga me za a iya tsinta daga ciki.
Mu soma da wadannan baitocin da ke nuni da tashi in taimake ka!
 
Tashi ka motsa ka bar nan wurin,
Gida ne na tsoro da halin tsiya.
 
Ka nemi wadata cikin duniya,
Akan kama zomo da son juriya.
 
Kasan duk wahala takan zan gudu,
Sauki yakan zo bayan shan wuya.
 
Wurin duk da an kaddara mutuwar,
Mutum za ya komo ba ya tirjiya.
 
Ina gargadin ka a kan sirrukanka,
Ka boye su gam-gam cikin zuciya.
 
Ka duba alamu na karfinsu ne,
Da dai-dai da dai-dai duka sun mace.
 
Kai mai karatu a nan gun tsaye,
Ka dubi sadaukan ga duk sun wuce.
 
Shiga daga ciki ka dau darasi,
Na mazan jiyan nan da duk sun mace.
 
Mutuwa ta riske su babu shiri,
Ta murde ta watsar kamar dai a ce.
 
Ba su taka doro na wannan kasa ba,
Kamar masu cin kasuwa sun wuce.
 
Darussan da ke kunshe a cikin wadannan baitoci ina jin ba sai an yi musu fashin baki ba. Al’amari ne da muke ta tashi-fadi kansa. Dubi kuma wani rubutu da aka yi a jikin wani kabari da ake bayar da labarinsa a cikin littafin. Aka ce:
 
A cikin wannan fada mutum nawa ne kake tsammani sun rayu kuma sun mace. Yi kokari ka bar wa ’yan baya abin gani, lokaci ba ya jira kafin ka farga ya tafi. Sun ji dadi sun mori rayuwarsu cikin duniya, mutuwa ta dauke su ta maishe su kasa. Sun ci sun sha mai kyau lokacin rayuwa, sun mutu sun rube, sun zan abincin tsutsa.
 
Haka kuma idan isa da iko da tara dukiya ce abin tokabo, saurari wadanda suka taka tudun mun tsira, me suka ce? Ga jawabin da wani hamshakin mai mulki da dukiya ya yi nan, ya ce a rubuta shi a jikin kabarinsa, don darasi ga na baya, cewa ya yi:
 
Yaki nawa na yi? Askarawa nawa na kashe? Sau nawa na yi nasara? Sau nawa na fadi? Wane irin abinci ne ban ci ba? Wane irin abin sha ne ban sha ba? Wace irin waka ce ban ji ba? Wace irin rawa ce ban gani ba? Wadanne irin mata ne ban mallaka ba? Sau nawa ina yin umurni? Sau nawa ina yin hani? Fadoji nawa na mallaka? Gidaje fa, su ma nawa na mallaka? Na rusa birane, na tara bayi da kuyangi, a cikin fadata suke duk zagaye da bangwaye. Wannan duk a cikin jahilcina ne domin neman mulki da son tara dukiya. Ka yi tunani ya kai dan Adamu mai hankali, kada ka manta dole za ka sha daga kaskon mutuwa. Tana nan kusa tamkar kurar nan da ke kanka, kwaram ba zato ba tsammani sai dai ka ji ka a rami.
 
Shin irin wannan da masu mulkinmu da sarakuna da tajirai za su karanta ba za su karu ba? Ba za su hankaltu ba?
 
Ga abin da ya kara jaddadawa domin mai karatu, ya ce:
 
Ya kai wannan mutum da ka tsinci kanka a cikin wannan fada, ga gargadi zuwa gare ka: Kada ka shagala da al’amurran duniya, kada ka bari dadin cikinta ya rude ka, kada kuma ka bari wahalarta ta zautar da kai. Ka sani dadin duniya ba mai dorewa ba ne, haka ma wahalarta ba ta dorewa har abada. Duk abin da ka samu a cikinta tamkar bashi ne ka karbo, a kowane lokaci mai bashin nan zai iya karbe abinsa. Abin da duk ka gani cikin duniya tamkar mafarkin mai mafarki ne, kai, tamkar gulbin hamada ne ga mai jin kishirwa. Shaidan ke kawata maka duniya, kana ganinta tamkar wata Aljanna, ba tare da ka farga ba har mutuwa ta riske ka. Kada ka yarda da duniya domin ita budurwar wawa ce, takan daga mutum sama daga karshe idan ya sakankance da ita sai ta sako shi kasa. Kada ka yarda da rudinta, kada ka yarda da zugar shaidani.
Misali na rayuwata kadai ya ishe ka gargadi; na mallaki garke dubu bisa dubu na dawaki, na mallaki babbar fada. Ina da mata da sa-daka guda dubu kyawawan gaske kamar watanni, dukkaninsu kuma ’ya’yan sarakuna ne. Ina da ’ya’ya dubu, dukkaninsu zakokin yaki ne. Na shekara dubu ina mulki kamar ba zan mutu ba. Na mallaki dukiya wadda ba ta da adadi kamar kasa, babu wani sarki da ya tara irin dukiyar da na tara a lokacina. Na shagala da rayuwa har ina ganin kamar ba zan mutu ba. Kwaram, babu zato babu tsammani sai mai katse jin dadi ta auka mini, mai raba da da mahaifi, mai raba mata da miji, mai raba tajiri da dukiya, mai rushe gidaje da birane, mai dauke babba da yaro, mai raba uwa da jariri. Mara tausayin talaka don talaucinsa, mara tsoron sarki da tajiri don karfinsu.

Za mu ci gaba