✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat (4)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen labarin da muke kawo muku makonnin uku da suka gabata:“A yanzu wannan ya wuce,…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen labarin da muke kawo muku makonnin uku da suka gabata:
“A yanzu wannan ya wuce, ina so ka mayar da ni mace, ka rika ba ni lokaci, idan ka fita ka rika dawowa gida da wuri saboda ta haka ne za ka fahimce ni sosai, ka san matsalolina na san naka, na san abubuwan da kake so da kuma wadanda ba ka so, idan wani abu na damun mu sai mu tattauna da yadda za a shawo kan duk wani abu da zai kawo tarnaki a cikin rayuwar aurenmu. A gaskiya ni mace ce mai son kulawa, ina so a dauke ni da mahimmanci. Ina da shagwaba da kwarkwasa da kuma kisisina.  Idan na yi kwalliya ina so a rika yabawa, haka idan na yi girki idan ya yi dadi a yaba mini, haka idan bai yi ba a fada mini cikin hanyar da zan fahimta. Kada idan girkin bai yi dadi ba ka boye, ko kuma ka rika fushi. Ni mace ce mai son a fada mini gaskiya. Idan na yi maka laifi ka fada mini zan ba ka hakuri. A yanzu ina so ka fada mini abubuwan da kake so da wadanda ba ka so.”
“Bayan ta yi shiru ne sai na ci gaba da magana, ina so ki rika yi mini uzuri. Kada ki rika saurin fushi, sannan idan na yi miki abin da ba daidai ba, ki sanar da ni ta hanyar aminci. Ina da saurin fushi, amma idan kuma aka ba ni hakuri ina da saurin saukowa. Ina so a rika lura da ni kamar kwai.  Ba na son kananan maganganu.”
“A nan muka dauki alkawarin duk abin da ya faru za mu tattauna don samo bakin zaren matsalar. Tun daga wannan lokaci duniyar rayuwar aurenmu ta dawo sabuwa gagal a leda. Muka dauki alkawarin kare soyayyarmu ta sama-da-kasa da kuma gefe da gefe.” Ya yi shiru sannan ya ci gaba da numfashi a hankali.
Daga nan na fuskanci Hafsat, a lokaci guda na tambaye ta ko tana da karin bayani, sai ta ce mini babu, ai tuni mijinta Kabir ya fadi komai da komai, sai dai ta roki na taya su addu’a don su fi karfin shaidan ko da gaba ya sake kawo musu bara.
A cikin jawabin nata ne wani abu ya tsaya mini a rai: “Tun bayan da muka kawo karshen matsalolin da suka yi cacukwi da rayuwar aurenmu, sai na samu natsuwa da kwanciyar hankali, na kuma samun tabbacin lallai aure rahama ne. Ina kara mika godiyata ga mijina, domin a yanzu ya zama garkuwa a gare ni, ya zama madagora a gare ni, ya zama ginshiki a gare ni, ya kuma zama wani sinadari da ke sanya rayuwata armashi. Mijina yana taimaka mini wurin lura da yara, a gabanka ka ga ya yi musu wanka, yana taimaka mini a kicin, inda idan ba ni da lafiya ko ma ina da lafiya yakan shiga kicin ya girka mana abinci. Ranar Asabar ko Lahadi idan yana gida tare muke share gida, mu wanke bandaki, mu gyara falo da dakin kwananmu, mu yi dukkan aikace-aikacen gida. Allah Ya saka masa da alheri.”
Wannan ne ya tabbatar mini tattaunawa tsakanin ma’aurata na da matukar mahimmanci, za ta kuma inganta hade da kara dankon aure. Don haka nake fatan ma’aurata da kuma wadanda za su yi aure gaba su yi amfani da darussan cikin labarin nan. Allah Ya taimake mu, amin.