Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku:
Bayan Kabir ya fuskance ni sai ya ci gaba: “Mun dauki lokaci a haka wanda kai shaida ne kan abubuwan da suka faru, tun da ka yi mana nasiha sau fin shurin masaki. Rayuwar aurenmu ta yi bikikkirin, muka kuma rasa inda za mu sa kanmu. Ta daina yi mini girki, ni kuma na daina zama a gida, har sai na ga dama nake dawowa. Dukkanmu muka rika jin girman kan mu tuntubi juna don kawo karshen al’amarin. Abin mamaki shi ne, duk da zaunar da mu da kake yi hade da yi mana nasiha hakan bai sanya shaidan ya rabu da mu don mu fahimci juna ba, sai wata rana da rashin lafiya ta kama ni, lokacin da na yi fama da amai da gudawa. A nan na lura ashe boyewa kawai take yi don ta nuna mini ruwa ba sa’an kwando ba ne.” Ya tsahirta, sannan ya gyara zama, hakan ya sanya na gyara zama, a lokaci guda na ci gaba da kallonsa, daga baya kuma na fara magana.
“Yanzu dai wannan ya wuce, yaya aka yi rayuwarku ta samu sabon babi na aminci, jin dadi da kuma kwanciyar hankali?”
Ya mike tsaye muka bi shi da kallo, ya fara takawa har ya zauna kusa da Hafsat. Bayan ya kalle ta ne, sai kuma ya fuskance ni, daga bisani ya ci gaba da magana: “Bayan na samu sauki an kuma dawo da ni gida, sai na ga ta ci gaba da kula da ni, za ta dafa mini abinci da sauran abubuwan da nake bukata. Daga nan sai na yi tunanin mene ne amfanin rashin zaman lafiyar da muke yi? Shin ba auren soyayya muka yi ba? Idan haka ne me ya sa muke zaman doya da manja? Baya ga haka idan muka rabu mene ne makomar ’ya’yanmu? Daga nan sai na ji jikina ya yi sanyi domin na gane shaidan ne yake yi mana fitsari hade da yi mana mummunar huduba don ya farraka mu. Ai sai na yi alwashin yin duk abin da zan yi don ganin komai ya fara tafiya daidai a gidana.” Ya sake yin shiru, amma daga bisani ya ci gaba.
“Wata rana tana zaune a falo tana kallo sai na iske ta. Da ganin yadda na tunkare ta ta fahimci na zo da batu mai mahimmanci. Hakan ne ya sanya ta mike sannan ta nufi inda talabijin yake, inda bayan ta isa ta rage sautin talabijin din, sannan ta dawo ta zauna. Bayan ta zauna ta kuma fuskance ni hade da tattara hankalinta gare ni, sai na yi gyaran murya, daga nan na fara magana: dukkanmu ba yara ba ne kuma mun san abin da ya dace da wanda bai dace ba. Ta gyada kai. Kamar yadda dan kwairo ya fada ne, kowag gyara ya sani haka kowab bata ya sani. Ba sai na koma baya don tuna mana bakaken abubuwan da suka faru a a bakaken ranakun da suka wanzu a tsakaninmu ba, dukkanmu ba mu kyauta ba, don haka ne nake so mu kawo karshen wannan abun da ke faruwa. Fada mini abubuwan da ki ke so na rika yi miki da wadanda kuma ba kya so, ta haka ne za mu gudu tare mu kuma tsira tare.” Ya sake yin shiru, ya kalle ta kafin kuma ya kalle ni.
“Daga nan ne na lura da jikinta ya mutu, inda kuma bayan wani lokaci sai ta fara magana: A lokutan baya na yi zargin ba kya kyauta mini, ka dauke wata bola da ba ni da daraja ballantana kima. Shaidan ya raya mini ni ma ‘yar boko ce na kuma yi digiri, ya rika raya mini karfina ya kai, ina kuma da ‘yancin yin abin da na ga dama ba tare da wani ya hana ni ba. Da wannan ne na fara yi maka abin da na ga kai ma ba za ka ji dadi ba. Sai na yi tunanin na nemi sulhu sai kawata ta rika karfafa mini gwiwa a kan kada na ba da kai bori ya hau.”
Za mu ci gaba insha Allahu
Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat (3)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku:Bayan Kabir ya fuskance ni sai ya ci gaba:…