✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasin rayuwa daga labarin yaro mai amana

Mun samu gudunmuwar labarin nan daga zakakurin marubuci kuma masani, Malam Nasir G. Ahmad (08065496902). Mu nazarci labarin kamar haka: An yi wani mawadacin mutum…

Mun samu gudunmuwar labarin nan daga zakakurin marubuci kuma masani, Malam Nasir G. Ahmad (08065496902). Mu nazarci labarin kamar haka:

An yi wani mawadacin mutum mai suna Abu Habib, mutumin kasar Magrib, wanda daga baya duniya ta juya masa daya shafin nata, dukkan kadarori da tsabar kudin da ya mallaka suka kare.
Wannan mutum, wata rana yana zaune yana tunani sai ya furta cewa:
“Yayin da duk harkokina suka sukurkuce sai na wayi gari ba ni da komai, daga gidan da nake ciki sai wata amintacciyar kuyanga tawa. Ganin haka sai na sayar da gidan nawa dinare dubu, na dauki kuyangata muka shiga ayarin matafiya zuwa birnin Makka. Na ce da ita, ‘Rike wannan kudin a wajenki, ki yi damara da su.’
Matar tawa sai ta zamo idan mun sauka a zango sai ta haka rami cikin hemarta ta binne kudin. Da ta ji shelar tashi sai ta hako su ta ci damara da su, sannan ta fito mu tafi.
“Wata rana muka tashi daga wani zango kusa da wani gari sai ta manta kudin a karkashin kasa ba to tono su kamar yadda ta saba ba, har muka yi nisa. Da ta fada min sai hankalina ya yi matukar tashi, na rasa abin da ke min dadi a duniya. Haka na hakura muka ci gaba da tafiya.
“Yayin da muka isa Makka sai na shiga tunanin na sayar da wannan kuyanga tawa, amma zuciyata ta ki amince min da hakan, har muka gama aikin hajji muka dauki hanyar komawa gida.
“Muna nan tafe har muka sake yada zango a wannan gari, inda na bar dukiyata. Sai na fita neman wurin da muka sauka a lokacin tafiyarmu. Babu komai a wurin daga rairayin hamada sai wani yaro tare da tumakinsa yana kiwo. Na isa wurin ina ta dube-dube a kasa. Yaron ya ce da ni, ‘Kai kuwa me kake nema a wannan wuri haka?’
“Na ce, ‘Wani abu na binne a wannan wuri.’
“Ko za ka siffanta min shi, in ga ko na sani?’ Yaron ya ce da ni.
“Ni kuwa na ce da shi, karamar jaka ce mai launin ja, tana kunshe da dukiya.’
Yaron kawai sai na ji ya ce mani: “Me ke gare ni daga ciki idan na nuna maka inda wannan dukiya taka take?”
Ni kuwa sai na ce masa: “ Zan raba dukiyar biyu na ba ka rabi.”
Jin haka, sai yaron nan ya nuna mini wani wuri da hannunsa, ya ce: “Ga ta can, je ka tono ka dauka!”
“Nan take sai na rude. Na tsammaci ko ba’a yake yi min. Da ya ga haka sai ya je da kansa ya tono jakar ya kawo, ya ajiye ta a gabana.
“Na yi godiya ga Allah. Na fitar da kudin na raba biyu daidai, na ce ya dauki kashi guda.
Shi kuwa sai ya ce: “Ina ganin rabin ma ya yi yawa. Rabin rabi ma ya ishe ni.”
Na dauki kashi guda na raba shi biyu na ce, ‘Bismilla.’
Maimakon ya amsa, sai ya ce mani: “Rabin rabin ma, kara kasa shi biyu na dauki guda.”
Na kuma daukar rabin rabin na raba shi biyu, na ce ya dau tumunin da ya bukata.
Yaron nan ya dube ni ya ce: “Amma lamarinka na da ban mamaki. Na ki dauka baki daya saboda bai halatta gare ni ba. Na kuma bar rabinsu yayin da ya halatta gare ni, sannan ka yi tsammanin zan iya karbar wani abu daga ciki? dauki dukiyarka ka tafi.”
Na ce da shi: “Kai kuwa da kake ko bawa?”
Ya ce: “Ni bawa ne.”
Na ce masa, bawan wane ne shi?
Ya ce: “Ni bawa ne ga shugaban dattijan wannan garin.”
Jin haka, ni kuwa sai na shiga cikin garin na iske dattijon nan zaune, mutane na kewaye da shi.
Bayan mun gaisa na ce da shi na ga wani yaro yana kiwon tumaki a bayan gari. Bukatata ita ce ka sayar min da shi.
Da dattijon ya ji haka, sai ya sanar da ni cewa: “Dinare goma na saye shi.” Ni kuwa na ce da shi na saye shi dinare ashirin.
“Idan ban sayar da shi dinare ashirin din ba fa?” Abin da ya gaya mini ke nan.
Na ce masa: “Idan haka ta faru sai na biya ka dinare talatin.”
Ya dubi mutanen da ke kewaye da shi ya ce: “Kuna jin abin da yake cewa? To wai kai me ya ja hanakalinka game da yaron ne da kake son sayensa bisa wadannan makudan kudi?”
Na ba shi labarin duk yadda muka yi da yaron, sannan na ce: “Don haka ne na yanke shawarar sayensa, domin na ’yanta shi, na kuma sayi dabbobin da yake kiwo na mallaka masa su.”
Shugaban nan ya ce: “Saboda abin alheri daya tak da ya yi maka kake son saka masa da wannan tagomashi? To mu kuma tun lokacin da muka mallake shi yake yi mana abin alheri a kullum. Don haka mu muka fi ka cancantar mu saka masa. Jama’a ku shaida cewa daga yau na ’yanta shi saboda zatin Allah. Na kuma mallaka masa dabbobin da yake kiwo!”
“Dadi ya kama ni. Na tafi cike da farin cikin samun biyan bukatata.”
***
Jama’a, kadan ke nan daga alheran da mai rikon amana zai iya samu a rayuwar duniya, kafin kuma gwaggwaban alherin da zai gamu da shi a lahira. Allah Ya ba mu ikon rike amana, amin.