Da ranar kai wa Dokta Ibrahim ziyarar yi masa ta’aziyya ta zo ne sai Dokta Samira tare da mahaifiyarta da wadansu kannenta biyu suka shirya inda direban gida ya dauke su zuwa garin su Ibrahim.
Sun isa garin da misalin karfe 11 na safe, sai dai Samira ba ta san ainihin gidan su Ibrahim ba, don ko lokacin da suke makaranta ba ta taba zuwa garinsu ba balle ta san gidan. Daga nan suka yanke shawarar samunsa a asibitin da yake aiki da yake asibitin ba boyayye ba ne.
Da kwatance har suka isa asibitin su Dokta Ibrahim musamman ganin yadda ya yi suna a tsakanin mutanen gari saboda irin taimako da saukin kan da yake da shi.
Da isarsu asibitin suka nemi izinin ganin Likita Ibrahim inda aka ce su dan dakata don yana duba marasa lafiya a lokacin. Bayan an dauki dan lokaci sai aka yi musu iso. Shigarsu ofishinsa ke da wuya sai ya hada ido da tsohuwar budurwarsa Samira da kuma wadansu mutane da suka tare da ita wanda yake kyautata zaton iyalinta ne.
Nan murna ta kama shi, inda ya yi musu iso. Nan take Samira ta gabatar da mahaifiyarta da kannenta biyu ga Dokta Ibrahim kuma ta shaida masa sun zo yi masa ta’aziyya ne game da rasuwar matarsa, Halima.
Ibrahim da Samira da sauran iyalanta suka rankaya gidan su Dokta Ibrahim don yi wa iyayensa ta’aziyya.
Da suka isa gida ya gabatar da Samira ga iyayensa, inda ya sanar da mahaifiyarsa cewa Samira ita ce budurwar da suka yi soyayya a makaranta amma Allah bai nufi zai aure ta ba.
Hajiya Delu, mahaifiyar Ibrahim ta yi matukar murna da ta hadu da Dokta Samira. Kuma ta ji Samira ta kwanta mata a rai, amma ganin abubuwan da suka faru a baya ya sa ta danne, kuma a yanzu ba ta son tilasta wa Ibrahim sake aurar wata mace in dai ba shi ya gabatar musu da ita ba. Sun yaba masa a kan amincewa da auren dole da suka yi masa a farko, amma sun yanke shawarar kyale shi a karo na biyu ya nemo matar da yake so ya aura, don su ba shi hakkinsa, musamman ganin yanzu yana cikin wani yanayi na rasa Halima.
Nan mahaifiyar Samira da mahaifiyar Ibrahim suka shiga gaisawa da juna yayin da Dokta Ibrahim da Dokta Samira suka fita waje don su gana da juna.
Bayan sun kebe ne sai tsohuwar soyayya ta zama sabuwa. Dokta Ibrahim ya ba Samira labarin dukkan abubuwan da suka faru har ta kai aka yi masa aure da Halima. Hasali ma ya shaida mata duk da yake bai so auren ba, amma a karshe ya gamsu da zaman da suka yi da Halima. Ya ce a da ya dauka zai dauki lokaci mai tsawo kafin ya maye gurbin Halima, amma haduwar da suka yi da Samira ta sa ya canja shawara kan zai aure ta idan ta amince, don ba zai tilasta mata ba, kuma bai sani ba ko a yanzu tana soyayya da wani ba.
Dokta Samira ita ma ta ba shi labarin irin halin da ta tsinci kanta bayan ta samu labarin an yi wa Ibrahim auren dole. Kuma ta fawwala wa Allah komai sai ga shi cikin wata kaddara Allah Ya sake hada su. Nan take ta amince da bukatar Dokta Ibrahim ta nuna za ta aure shi.
Kafin Samira su bar gidan sai Dokta Ibrahim ya sanar da mahaifinsa Malam Usman cewa ya yanke shawarar ya auri Samira. Nan ma mahaifinsa ya sanar da matarsa Hajiya Delu inda dukkansu suka yi murna da jin wannan labari. Nan take aka shaida wa mahaifiyar Samira ita ma ta amince da niyyar idan ta koma gida za ta sanar da maigidanta da sauran ’yan uwa don a sanya ranar biki.
Za mu ci gaba insha Allahu
Za a iya samun Ahmed Garba a 08097015805