A ranar Ibrahim dai ya kwana ne a dakin ba tare da ya runtsa ko ya kula Halima ba saboda bakin ciki. Haka ya ci gaba da zama da amaryarsa Halima har na tsawon lokaci.
Halima kan yi duk mai yiwuwa don ganin ta faranta wa Ibrahim (angonta) rai musamman a bangaren yi masa girki da yi masa wanki da kula da tsabtar dakin da ma daukacin gidan ba tare da ta gajiya ba. A kullum takan ce wannan wata dama ce a gare ta ta samun lada a wajen Mahalicci idan ta bi mijinta sau-da-kafa. Sannan iyayen Ibrahim musamman mahaifiyarsa Hajiya Delu tana matukar alfahari da Halima ta wajen kyautata mata, saboda tunda Halima ta zo gidan ta karbe duk wani aikin gida har na dafa abincin gidan gaba daya.
A duk lokacin da Hajiya Delu ta nemi Halima ta huta sai ta nuna hakan ba zai yiwuwa a wajenta ba, ta kyale surukarta kuma tamkar mahaifiyarta tana aiki, yayin da ita kuma ta zuba ido tana kallo.
Gaskiya dabi’un Halima suna matukar ba iyayen Ibrahim sha’awa inda suka ci gaba da nuna godiyarsu ga Allah da Ya sa suka aurar da ita ga Ibrahim.
An dauki lokaci mai tsawo amma Ibrahim bai kula Halima ta bangaren kwanciyar aure ba. Hakan ya sa Halima ta kai kararsa wajen magabata inda maganar ta kai har kunnen mahaifinsa Malam Usman.
Daga nan ne Malam Usman ya sanar da Hajiya Delu halin da ake ciki. Ita kuma Hajiya Delu sai ta kira Ibrahim ta nemi jin dalilinsa na kin kula matarsa Halima.
Ta nuna bacin ranta game da abin da ya yi, bayan ta yi masa nasiha. Ta nuna masa illar rashin kula matarsa musamman ganin yarinya ce mai hankali.
Nan take Ibrahim ya yi alkawarin zai ci gaba da kula da matarsa kuma hakan ba zai sake faruwa ba saboda biyayyar da yake yi wa mahaifansa.
Daren da Ibrahim ya yi kwanciyar aure da Halima, matarsa sai ya ji a duniya babu wadda yake kauna fiye da ita. Sai Allah Ya sanya masa tsananin soyayyar da bai taba ji a rayuwarsa ba tun daga wannan lokaci.
Kafin lokaci kankane sai ango da amarya suka shaku da juna.
A baya ba tare suke cin abinci ba, amma tun daga ranar sai ya zama daya ba ya iya cin abinci sai dayan nan nan. Ke nan komai dare sai Halima ta jira angonta Ibrahim ya koma gida kafin su ci abinci tare.
Kafin wani lokaci, Allah Ya buda wa Ibrahim ya samu aiki a babban asibitin gwamnati da ke garinsu. Zuwa wani lokaci Dokta Ibrahim ya yi suna, inda kowa ya bude baki babu abin da yake yi masa sai addu’ar fatan alheri saboda kwazonsa da kuma iya tafiyar da jama’a.
Za mu ci gaba
Za a iya samun Ahmed Garba a 08097015805