✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dara ta ci gida

Wani magidanci ne da ya kware wajen neman mata a Facebook, rannan sai dara ta ci gida, wata diyarsa sai ta bude shafinta da sunan…

Wani magidanci ne da ya kware wajen neman mata a Facebook, rannan sai dara ta ci gida, wata diyarsa sai ta bude shafinta da sunan karya kuma ta sanya hoton dab a nata ba. Da ya ganta sai ya neme ta, ga yadda suka yi hira: Baba: “Assalamu alaikum.” Yarinya: “Wa’alaikumus salam.” Baba: “Yaya gida?” Yarinya: “Lafiya lau.” Baba: “Amma da alama ba mu taba gaisawa ba ko?” Yarinya: “Eh, wallahi; ka san abubuwan ne da yawa.” Baba: “Don Allah wane gari kike?” Yarinya: “Ni ’yar Hadeja ce.” Baba: “Ko za ki ba ni lambarki mu rika gaisawa?” Yarinya: “Ni bana bada lambata a Facebook.” Baba: “Saboda me?” Yarinya: “Haka nan.” Baba: “Kina so yau in kasa barci?” Yarinya: “Hmm, baba ke nan! Amina ce fa, wai ba ka gane ni ba?” Baba: Shiru, ba amsa.”