Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya ba Sarkin Dukku Haruna Kadir Rasheed Sandar girma.
Da yake jawabi kafin mika masa sandar, Gwamna Dankwambo ya ce sarakunan gargajiya su ne matattaran al’adun gargajiya da ba za su bari a manta da su ba.
Gwamnan ya taya shi murna da kuma yi masa addu’ar alheri da fatan Allah Ya shige masa gaba.
Sarki na biyu a kasar Dukku kuma Lamido na goma sha bakwai, an nada shi ne a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2013 bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Abdulkadir Haruna Rasheed Sarki na farko a kasar Dukku. Kafin nadin Alhaji Haruna Kadir Rasheed a matsayin Sarkin Dukku, kwararren ma’aikacin banki ne da ya yi aiki da Babban Bankin Najeriya CBN.
A jawabinsa bayan an mika masa sandar, Sarkin na Dukku ya gode wa Gwamnan Ibrahim Hassan Dankwambo wanda da taimakonsa ne aka gudanar da wannan biki na wankan Sarauta.
Ya ce shi a lokacin da aka nada shi sarki ya karbi abun da hannu bibiyu don sadaukar da kai wajen taimakon jama’arsa da ma Masarautar Dukku baki daya.
Da yake jawabi a wajen bikin, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya taya sarkin na Dukku da al’ummar Jihar Gombe murna na samun hazikin mutum a matsayin sarki.
Taron ya gudana ne a babban filin wasa na garin Dukku ya kuma samu halartar sarakuna da dama da suka hada da Sarkin Bauchi da Sarkin Ningi da Sarkin Shani da Sarkin Katagum da Sarkin Kaltungo da sauransu.