✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Danja da Mansura sun cika shekara 10 da aure

A ranar 14 ga Yuli, 2017 fitaccen mawaki da kuma jarumin fina-finan Hausa, Sani Musa Danja da kuma tsohuwar fitacciyar jaruma Mansura Isa suka cika…

A ranar 14 ga Yuli, 2017 fitaccen mawaki da kuma jarumin fina-finan Hausa, Sani Musa Danja da kuma tsohuwar fitacciyar jaruma Mansura Isa suka cika shekara 10 da aure.

a ranar 14 ga Yuli shekara ta 2007 ne masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood ta  gudanar da babban taro na musamman na auren jaruman, inda aka yi biki na kece raini da kuma kasaita.

A yanzu haka ma’auratan Allah ya azurta su da ‘’ya’ya hudu wadanda suka hada da Iman, sai Khalifa, sai Sultan sai kuma dan auta a halin yanzu wato Sudais.

A lokacin da Aminiya ta tambaye ta yadda take ji sakamakon yadda aurenta ya cika shekara 10 sai ta ce, “babu wani abu da zan ce sai godiya ga Allah da Ya azurta mu da ’ya’ya hudu, wato Iman da Khalifa da Sultan da kuma Sudais. Sirrin nasarar aurenmu tana wurin Allah, dalilin ibada da bauta ta sanya har yanzu muke tare, ba mu da wani buri face mu ci gaba da daukar nauyin ’ya’yanmu ta hanyar ba su ilimi da kuma kyakkyawar tarbiyya har su girma.”

Dangane da darasin da ta koya kuwa sai ta ce, ta fahimci cewa bayyana masoya ko ma’aurata suna son juna ba ya isa a aure, “aurena ya koya mana hakuri da juna da tausayin juna, sannan duk lokacin da wani abu ya faru sai mu kalli idon juna, sannan mu tuna irin soyayyar da ke tsakaninmu.”

Ta ce, ta fahimci duk yadda ka kai da kudinka duk matsayin da ka taka sai ka yi hakuri a batun aure, saboda bayan aure abubuwa da yawa canzawa suke  daga kyau, kudi, lafiya da sauransu, yanayin hakurinka shi ne yanayin dadewar aurenka.

Ta ce a yayin zaman aure dole mutum ya manta da wadansu abubuwa da suka faru, dole ya bata wa abokin zamansa rai, sannan dole abokin zamansa ya bata masa rai, amma sai a manta a kuma yafe, hakan zai sanya a samu zaman lafiya, don “haka na yi hakuri, na yi juriya, na kuma yi yafiya, inda a yanzu nake cikin nishadi da jin dadi a rayuwar aurena.”

“A cikin shekara 10, mun yi fada, mun yi kuka, mun yi hakuri da juna, wanda ga shi har yanzu muna tare, ya kamata a taya mu murna. Ina kaunarka sosai Sani Danja. Ina yaba maka da yadda ka yi hakuri da ni, da kuma yadda kake kambama ni.” Inji Mansura.

Tsohuwar jarumar ta kuma yaba wa Yakubu Muhammad da Samira Ahmad da Sadiya Gyale da sauran wadanda suka yi ruwa da tsaki yayin bikinsu, inda ta ce sai dai Allah Ya saka musu da alheri bisa gudunmuwar da suka ba su.

Ta ce ta tuna lokacin da aka yi baikonsu lokacin da abokan ango suka taka rawa, sun sha wahala sosai har zuwa lokacin da wadansunsu suka kwana a kasa.

A lokacin da Aminiya ta tuntubi Sani Danja kuwa sai  ya ce babu wani abu da ya fi so sama da iyalinsa, kuma kwanaki sun shude kamar kiftawar ido har aurensa ya cika shekara 10.

Jarumin ya yi addu’ar Allah Ya kara wa iyalinsa albarka, ya kuma sanya aurensu ya zama mutu ka raba takalmin kaza. 

“Ina kaunarki, ina darajaku, ina kuma addu’ar Allah Ya kara muku albarka, ya kara wa aurena albarka.”