✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dani Albes ya koma kungiyar Jubentus

dan kwallon kasar Brazil, Dani Albes ya koma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus da ke kasar Italiya daga kungiyarsa ta Barcelona da ke Spain.dan wasan…

dan kwallon kasar Brazil, Dani Albes ya koma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus da ke kasar Italiya daga kungiyarsa ta Barcelona da ke Spain.
dan wasan wanda ya shafe shekaru takwas yana buga wa Barcelona wasa, ya sanya hannu a takardar yarjejeniyar buga wa Jubentus wasa na shekara biyu.
dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa: “Ina matukar alfahari da farin ciki a matsayina na dan kwallowan da rayuwa ta ba ni damar buga wa babbar kungiyar kwallon kafa ta duniya.
Tuni dan wasan ya sauka a garin Turin da ke Italiya, inda aka gwada lafiyarsa sannan ya sanya hannu domin buga wa kungiyar kwallo har zuwa watan shida na shekarar 2018.
Albes ya buga wa Barcelona wasa inda ya lashe kofuna shida na rukunin La Liga sannan ya lashe kofuna uku na Zakarun Turai kuma ya buga wa kasarsa ta Brazil wasa har sau 93.