✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dangwari mai karya

Wani dangwari ne da ma al’adarsu ce idan an haifi yaro sai a rika koya masa karya. To akwai wani rafi kusa da inda ake…

Wani dangwari ne da ma al’adarsu ce idan an haifi yaro sai a rika koya masa karya. To akwai wani rafi kusa da inda ake zuwa koya wa yaro karyar. Sun kama hanya zuwa ke nan, sun zo tsallaka rafin sai baban ya buga ihu ya ce: “Kai, kai yaro, na taka kifi.” Sai yaron ya kada baki ya ce: “Lallai shi ya sa na ji maikon kifin a bakina.” Sai baban ya ce: “Ah, ah, lallai yaro ka yi nisa, bari mu koma gida.”
Daga Iliyas Idris Fahad Suleja